Jama'a kuyi hukunci: Wani matashi ya yi barazanar daburta shafin Legit.ng saboda zargin muna kushe shugaba Buhari

Jama'a kuyi hukunci: Wani matashi ya yi barazanar daburta shafin Legit.ng saboda zargin muna kushe shugaba Buhari

Jama'a ku yi mana shari'a; Wani matashi mai akwatin sakon <sender@5ymail.com> ya turo mana wasikar ta akwatin sakonmu cewa idan ba muyi hattara ba, shafin daburta shafinmu kamar yadda ya daburta na wasu, a ikirarinsa.

A lokuta da dama, mu kan samu irin wadannan sakonni daga bangarori gudu. Wasu na cewa mun fiye wallafa muradun gwamnati, wasu kuma suce muna kushe gwamnati; amma a matsayinmu na yan jarida, aikinmu mukeyi kuma babu ruwanmu da siyasa.

Yace: "Zamu daburta shafinku bisa ga kushe gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari."

"Mun lura da cewa kuna yawan sukar gwamnatin Baba Buhari, a saboda haka mun yi hacking dinku, kowa na iya shiga shafin ku ta www.nishadi.tv free, kuma mun hargitsa code din taku, matsiyata.

Ku kuma mara sa goyan Baba Buharin namu (4+4) ko kun ki, za mu yi hacking din ku, kun san kan ku irin su Nishadi Tv, northern Habiscus, Jaruma, Hausa Fulani da sauransu.

A fadi wa Nazir Sarkin Waka mun gano kana da fuska biyu amma muna sane da kai, in ma kai ka ke goyan bayan yan Nishadi TV ka ja kunen su.

Yanzu haka mun yi hacking din NishadiTV yanzu webside dinsu free ne idan kana tantantama shiga www.nishadi.tv je ku, ku sha kallo free a banza.

Masoyin Baba Buhari har abada 4+4."

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya dira jihar Enugu (Bidiyo)

Jama'a kuyi hukunci: Wani matashi ya yi barazanar daburta shafin Legit.ng saboda zargin muna kushe shugaba Buhari
Jama'a kuyi hukunci: Wani matashi ya yi barazanar daburta shafin Legit.ng saboda zargin muna kushe shugaba Buhari
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng