INEC ta diba ma’aikatan wucin gadi 814,453 domin zabe
- Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa ta kammala tantancewa da diban ma’aikatan wucin gadi 814,453
- Wadannan ma’aikata na wucin gadi da aka diba sune za su gudanar da zaben kasar da za a fara a watan gobe
- Shugaban hukumar yace an kammala duk wani tanadi na risit da kuma rabon muhimman kayayyaki
Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa ta kammala tantancewa da diban ma’aikatan wucin gadi 814,453 domin zaben kasar mai zuwa.
A cewar hukumar, an kammala duk wani tanadi na risit da kuma rabon muhimman kayayyaki.

Asali: Facebook
Shugaban hukumar zaben, Farfesa Mahmoud Yakubu ya bayyana hakan a jawabinsa ga majalisar kasar a fadar shugaban kasa, Abuja a ranar Talata. An kuma bayar da kwafin jawabin ga yan jarida a ranar Laraba, 23 ga watan Janairu.
KU KARANTA KUMA: Mutanen Ebonyi za su fito su tarbi Buhari idan ya zo kamfe – Gwamna Umahi
Hukumar ta tuna cewa an ci gaba da yiwa masu zabe rijista a tsakanin ranar 27 ga watan Afrilu, 2017, da 31 ga watan Agustan, 2018 a ofishohinta da ke kananan hukumomi 774 da cibiyoyin da aka tsara a fadin kasar kamar yadda doka ta tanadar.
A wani lamari na daban, mun ji cewa hukumar zabe na kasa watau INEC ta bayyana cewa Alhaji Abdulfatah Ahmed ne ‘dan takarar da ta sani na kujerar Sanatan Kudancin jihar Kwara. INEC tace gwamnan ne zai rikewa PDP tuta a zaben 2019 da za ayi ba kowa ba.
Malam Garba Madami wanda shi ne babban kwamishinan zabe na INEC na REC a jihar Kwara yayi karin haske game da takarar Sanatan jihar. Madami yace Abdulfatah Ahmed ne ainihin ‘dan takarar Sanatan PDP da su ka sani.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng