Gwamnatin Buhari za ta kara adadin masu cin gajiyar N-Power zuwa 1,000,000

Gwamnatin Buhari za ta kara adadin masu cin gajiyar N-Power zuwa 1,000,000

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyan cewa gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kuduri fadada yawan yan Najeriya dake cin gajiyar tsarin tallafi na N-Power daga 500,000 zuwa 1,000,000.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Osinbajo ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu, yayin da yake gabatar da jawabi a wani taron sauraron ra’ayi da al’ummar garin Remoland suka shirya a fadar Akarigbo dake cikin garin Sagamu na jahar Osun.

KU KARANTA: Tsohon shugaban TETFUND ya nemi a yanke masa hukuncin kisa idan an kamashi da laifin rashawa

A jawabinsa, Osinbajo yace gwamnatinsa ta yi kokarin taka ma matsalar rashin aikin yi burki ta hanyar bullo da tsarin N-Power, Tradermoni, da kuma Marketmoni, dukansu tsare tsare ne na tallafi ga matasa da kuma kanana da manyan yan kasuwa.

Haka zalika ya kara da cewa gwamnati ta tattatara bayanan yan kasuwan garin Remoland gaba dayansu a karkashin tsarin Marketmoni, don haka yayi kira garesu dasu tabbata sun shiga an dama dasu a duk lokacin da aka sake bullo da wan tsarin tallafi.

Sai dai da wani ya tambayeshi akan yaushe gwamnati zata gina musu filin sauka da tashin jiragen sama da za’a dinga shigowa tare da fitar da kayan yan kasuwa, musamman amfanin noma zuwa kasashen waje, sai yace ba hurumin gwamnatin tarayya bane gina irin wannan tashar jirgin saman, aikin jaha ce.

“Na tabbata jama’an Remoland sun shaida ayyukan gwamnatin tarayya a garinsu, kuma a shirye muke mu kara wasu ayyukan, a yanzu haka muna gina hanyar Ikorodu/Sagamu, hanyace mai matukar muhimmanci wanda idan aka kammala shi za rage cunkoson ababen hawa akan titin.

“Zamu kawo muku ofishin hukumar kula da shige da fice ta kasa da zata dinga samar muku da sabon fasfo na yin tafiye tafiye, don haka ba sai kuna cigaba da zuwa Legas ko Osogbo ba kafin ku samu damar yin fasfo ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng