Yanzu Yanzu: Yan Shi’a sun toshe mashigin majalisar dokokin kasar

Yanzu Yanzu: Yan Shi’a sun toshe mashigin majalisar dokokin kasar

- Mambobin kungiyar yan Shi’a sun toshe babban mashigin majalisar dokokin kasar

- Yan Shi'an na zanga-zanga ne akan ci gaba da tsare shugabansu Ibrahim Zakzakky

- Shugaban nasu dai da matarsa na kulle kusan kimanin shekaru uku da suka gabata

Mambobin kungiyar yan uwa Musulmi na Shi’a sun toshe babban mashigin majalisar dokokin kasar.

Mambobin kungiyar na zanga-zanga ne akan ci gaba da tsare shugabansu Ibrahim Zakzakky.

Daruruwan yan Shi’an sun kai zanga-zangar nasu ne majalisar dokokin kasar, lamarin da ya tursasa jami’an tsaro da ke gadin yan majalisar dokokin rufe kofa.

Yanzu Yanzu: Yan Shi’a sun toshe mashigin majalisar dokokin kasar
Yanzu Yanzu: Yan Shi’a sun toshe mashigin majalisar dokokin kasar
Asali: Facebook

A baya mun dai ji cewa yan shi'ar sun a sahu inda suka yi kabbarar Sallah suna addu'o'i ga gwamnatin ta tarayya.

A farkon makon nan ne kotun dake sauraron karar da gwamnatin jihar Kaduna tashigar ta hana bada belin shi malamin na su, Shaikh Ibrahim Zakzaky da matarsa don samun damar neman lafiya.

KU KARANTA KUMA: Mambobin APC sun bawa hammata iska a harabar wata kotun tarayya

Tun farko dai, Lauyan su Shaikh Ibrahim Zakzaky da matarsa ya shaidawa kotun cewa “idon Shaikh Zakzaky daya tuni ya lalace sannan wanda ya ragema yana kan tabuwa, kuma matarsa akwai harsasai a jikinta wandanda ba'a cire ba."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng