Da duminsa: Buhari ya dira birnin Shehu, jihar Sokoto

Da duminsa: Buhari ya dira birnin Shehu, jihar Sokoto

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira jihar Sokoto domin yakin neman zabensa karo na biyu. Jirgin shugaban kasa ya isa filin jirgin saman Sultan Abubakar ne misalin karfe 10:05.

Manyan jami'an gwamnatin jihar Sokoto sun tarbi shugaba Buhari yayinda ya da sauka. Daga cikin wadanda suka tarbesa sune gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon gwamnan jihar, Ahmad Sani Yarima; ministan harkokin mata, Aisha Abubakar da sauran manyan jiga-jigan jam'yyar APC.

Daga saukarsa, shugaban kasan ya garzaya fadar mai alfarma sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad, domin kai masa gaisuwar ban girma.

Bayan gaisuwar, shugaban kasa zai tafi farfajiyar Shehu Kangiwa, domin yakin neman zaben 2019.

Daga jihar Sokoto kuma zai koma jihar Kebbi kamar yadda aka shirya, sannan ya koma birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: NFIU na cigaba da gano makudan kudin da Onnoghen ya dankare a bankin waje

Mun kawo muku da safen nan cewa jirgin shugaba Muhammadu Buhari ya tashi daga babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe Abuja zuwa jihar Sokoto da Kebbi domin gudanar da yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng