Aiki da cikawa: Wannan watan ne ‘yan sanda zasu fara jin alat mai kauri a asusunsu
- Akwai alamu masu karfi da ke nuni ga cewa a mako mai zuwa za a fara biyan sabon karin albashin da Buhari ya amince ayi wa jami’an yan sanda
- Hakan duk don a karfafawa jami’an yan sandan gwiwar yin aiki yadda ya kamata ne a lokacin zabe mai zuwa
Akwai alamu masu karfi da ke nuni ga cewa a mako mai zuwa za a fara biyan sabon karin albashin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince ayi wa jami’an yan sanda a wata Nuwamban shekarar da ya gabata.
Hakan duk don a karfafawa jami’an yan sandan gwiwar yin aiki yadda ya kamata ne a lokacin zabe mai zuwa.
Jaridar Daily Indepedent ta rahoto cewa fadar shugaban kasa ta saki wasu kudade na musamman a makonni biyu da suka gabata domin yin biyan.

Asali: Facebook
Amma an tattaro cewa kudaden da aka saki da farko ba zai isa a biya kanana da manyan jami’ai ba, don haka hukumomin yan sanda sun aika wasika ga fadar shugaban kasa inda suka nemi Karin kudade don biyan jami’an.
KU KARANTA KUMA: Yayi matukar wahala aiki tare da tsohon IGP – Inji Minista Dambazau bayan ritayan Ibrahim Idris
An kuma tattaro cewa sabon Karin albashin da shugaban kasa Buhari ya sanar bai kamata a biya ba har sai an amice da kasafin kudi 2019 sannan a saki kudade ga ma’aikatu da sassa daban-daban.
Hakan ya kasance ne saboda Karin albashin baya cikin kasafin kudin 2018 na yan sadan.
Amma bincike ya nuna cewa fadar shugaban kasa ta yi tunanin cewa idan aka yi Karin sabon albashin kafin zabe, musamman a wata Janairu zai karfafa gwiwar jami’a yan sanda wajen yin zabe da kyau.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng