Idan aka yiwa APC hisabi, shugabanninta a wuta za a jefa su

Idan aka yiwa APC hisabi, shugabanninta a wuta za a jefa su

- Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa jam’iyyar APCza ta shiga wuta idan da za a yi mata hisabi

- Obasanjo ya soki shugaban kasa Muhammau Buhari akan zargin cewa yana la’akari da kabilanci wajen nade-naden mukamai

- Yace idan shugaban kasar bai yarda da mutanen sauran kabilu ba wajen bayar da mukamai, toh kada ya nemi kuri’unsu a zabe mai zuwa

Tsohon shugaban kasa Olusegun 0basanjo ya bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki za ta shiga wuta idan da za a yi mata hisabi.

Obasanjo ya fadi hakan ne a wani hira da BBC a harshen Yarbanci.

Tsohon shugaban kasar ya soki shugaban kasa Muhammau Buhari akan zargin cewa yana la’akari da kabilanci wajen nade-naden mukamai.

Idan aka yiwa APC hisabi, shugabanninta a wuta za a jefa su
Idan aka yiwa APC hisabi, shugabanninta a wuta za a jefa su
Asali: UGC

Yace idan shugaban kasar bai yarda da mutanen sauran kabilu ba wajen bayar da mukamai, toh kada ya nemi kuri’unsu a zabe mai zuwa.

Obasanjo yace, “Idan muna Magana game da zunubai, mutanen da suke wajen a yanzu, idan muka yi masu hisabi, wuta za su shiga.

KU KARANTA KUMA: Kamfen: Yakin neman zaben Atiku a jihar Imo ya yi armashi (hotuna)

“Ba wai kurkuku kadai za a tura su ba, wutan jahannama za su shiga, duk wanda Allah ya boye laiukasa, toh an kare sirrika mai shi.

“Ban ce idan Atiku yaje wajen zai yi kamar Annabi Isah ko Annabi Mohammed ba, amma zai yi fiye da abunda muke gani a yanzu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng