Ku bar Najeriya ko kuma ku dandana kudarku – Yan sanda ga masu luwadi da madugo

Ku bar Najeriya ko kuma ku dandana kudarku – Yan sanda ga masu luwadi da madugo

- Rundunar yan sandan Najeriya ta gargadi masu aikata luwadi da madugo

- Misis Dolapo Badmos ta bukaci masu luwadi da madugo da su bar kasar ko kuma su fuskanci hukuci

- Ta kuma yi kira ga ‘Yan Najeriya da su samo hujja akan yan luwadi da madugo sannan su gabatar da hujjar

Rundunar yan sandan Najeriya ta ja kunnen masu aikata duk wani abu da ya shafi madugo ko luwadi da su yi gaggawan barin kasar Najeriya ko kuma su hadu da fushin doka, cewa babu gurbin aikata irin haka a dokar Najeriya domin an haramta.

Jami’ar hulda da jama’a na yan sandan Zone 2, Misis Dolapo Badmos ta bukaci masu luwadi da madugo da su bar kasar ko kuma su fuskanci hukuci.

Ku bar Najeriya ko kuma ku dandana kudarku – Yan sanda ga masu luwadi da madugo
Ku bar Najeriya ko kuma ku dandana kudarku – Yan sanda ga masu luwadi da madugo
Asali: Original

Ta kuma yi kira ga ‘Yan Najeriya da su samo hujja akan yan luwadi da madugo sannan su gabatar da hujjar.

Badmos ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram.

Tace: “Idan kai dan luwadi ko madugo ne, Najeriya ba wajen zaman ka bane. Akwai wata doka da ta haramta tarayyar auratayya a tsakanin jinsi guda, sannan idan aka kama wata kungiya ta hakan hukuncin shi ne kusan shekaru 15 a gidan yari.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Tsoffin ma'aikatan kamfanin jiragen sama sun goyi bayan Buhari

“Don haka idan kai dan luwadi ne, ka bar Najeriya ko kuma ka fuslanci hukunci. Amma kafin kace akwai bukatar hakan? Ka san cewa duk wanda ya taka doka akan wani laifi zai fuskanci hukunci daidai da abunda ya aikata duk kankatar laifin kuwa."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng