Duk da an haramta masa shiga Amurka: Atiku ya kashe $1.1m domin kwana otel din Trump
- Atiku Abubakar, ya samu damar shiga kasar Amurka bayan da ya biya wani kamfanin sirri $1.1m, wanda ke da alaka da fadar shugaban kasar Amurka
- Sama da shekaru 12 ke nan Atiku Abubakar, wanda yake takarar kujerar shugaban kasar Nigeria a zaben ranar 16 ga watan Fabreru da ke gabatowa
- Wani makusancin fadar shugaban kasa, Brian Ballard, shine ya sanya hannu kan yarjejeniyar wakiltar jam'iyyar Atiku, PDP, a kan lada $1.1m kowacce shekara
Wani rahoto da Legit.ng ta samu daga kafar watsa labarai ta RawStory da ke Amurka, ya tabbatar da cewa tsohon shugaban kasar Nigeria, Atiku Abubakar, ya samu damar shiga kasar Amurka bayan da ya biya wani kamfanin sirri $1.1m, wanda ke da alaka da fadar shugaban kasar Amurka.
A shekarar 2004, shugaban kasa George W. Buhs ya sanya hannu a kan wata dokar shugaban kasa ta 7750 wacce ta haramtawa duk wani mutumi daga wata kasa shiga Amurka ma damar ana tuhumarsa da zargin cin hanci da rashawa.
Sama da shekaru 12 ke nan tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar, wanda yake takarar kujerar shugaban kasar Nigeria a zaben ranar 16 ga watan Fabreru da ke gabatowa.
KARANTA WANNAN: Da duminsa: Sabon rikici ya barke a jihar Anambra, an kona gidaje da gonaki

Asali: Twitter
A ranar Alhamis din da ta gabata, Abubakar ya samu masauki a babban otel din shugaban kasa Donald Trump da ke Washington, DC.
Wani kwararren mai shige da fice kuma makusancin fadar shugaban kasa, Brian Ballard, shine ya sanya hannu kan yarjejeniyar wakiltar jam'iyyar Atiku, PDP, a kan lada $1.1m kowacce shekara.
A makon da ya gabata tsohon sakataren watsa labarai Raj Shah, ya shiga tawagar Ballard.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng