Abinda ya sa nake goyon bayan Atiku - Obasanjo

Abinda ya sa nake goyon bayan Atiku - Obasanjo

Tsohon shugaba kasa, Olusegun Obasanjo y bayyana wasu dalilai da suka sanya shi marawa tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar baya duk da cewar a baya ya sha alwashin kin mara masa baya wajen neman shugabancin kasa.

Idan za ku tuna, Obasanjo ya zargi Atiku da aikata rashawa kafin daga bisani ya zo ya amunce masa akan kudirinsa na neman shugabancin kasa a 2019.

A wani hira da yayi da BBC, an tambaye shi kamar haka: "Yallabai a lokuta da dama kace ba za ka taba goyon bayan tsohon mataimakinka, Atiku Abubakar ba, ak burinsa na neman shugaban kasa, inda ka zarge shi da rashawa. Amma kwatsam a yanzu shi ne dan takarar da kake goyon baya, Shin me ya sauya yanzu kake goyon bayansa?"

Abinda ya sa Obasanjo ya gafarta wa Atiku
Abinda ya sa Obasanjo ya gafarta wa Atiku
Asali: Twitter

Obasanjo ya amsa da: "Ya kamata ‘Yan Najeriya su fahimta. Nayi bayani akwai abubuwa guda biyu ne da nake son fada; Atiku ba mai ceto bane ba tsarkakken mutum bane. Kuma an yi sa’a bai ce shi tsarkakken ba ne.

"Bai yi ikirarin kasancewa mai gaskiya na jabu ba. Ka gane!

"Yazo nan ya nuna nadama, ya tuba akan abubuwan da ya aikata a baya. Duk abubuwan da na ce akansa na nan haka na ce.

"Babu wanda ya zo ya kawo rudani a kansu. Na yi imani kuma ni Kirista ne, a koyarwar ubangii a addinina shi ne na yi yafiya, saboda kaima a yafe maka. Har aka ce idan baka yafe ba, baka da ikon ka roki Ubangiji ya yafe maka. Ni ma mai zunubi ne, don haka ina so Ubangiji ya yafe mani.

"Dan haka duk wanda ya bata mani ya zo da nadama yana so na yafe masa, dole in yafe masa. Wannan shine na farko.

KU KARANTA KUMA: TraderMoni: Osinbajo ya fadi dalilan da yasa Obasanjo ke sukar shirin

"Na biyu, zabin da ke gare mu a halin yanzu a yanayin Najeriya a 2019, tsakanin dan takarar APC ne da na PDP. Sauran jam’iyyu za su biyo bayansu ne ko kuma ma ba su da tasiri. Don haka idan APC ta kawo Buhari ita kuma PDP ta kawo Atiku, bisa abinda na sani game da Buhari da abubwan da yayi, tsananin tsabagen gazawarsa, da nuna son kai da amincewa da barna, da rashin aikata daidai da rashawa, da kuma rashin karfin jiki, da zuciya da kuma duka abubuwan Buhari idan ka hada da na Atiku. Nayi imanin cewar Atiku zai fi iya aiki sau biyu akan Buhari.

“Kalli sha’anin Boko Haram , sha’anin tsaro, Boko Haram na barna fiye da kowanne lokaci. Sun hade da dakarun kasashen wae a yanzu. Suna kara karfi da kudin fansar da suke nema kuma ake biya."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng