Zaben 2019: Atiku Abubakar ya yi taron Allah-tsine-uwar-mai-karya a jihar Jigawa

Zaben 2019: Atiku Abubakar ya yi taron Allah-tsine-uwar-mai-karya a jihar Jigawa

Dan takarar kujerar shugabancin kasar Najeriya a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yayi taron Allah-tsine-uwar-mai-karya a jihar Jigawa dake zaman jiha daya daga cikin jahohin Arewa maso yammacin Najeriya.

Mun samu cewa dai dubun dubatar al'umma ne masoya dan takarar da kuma jam'iyyar ta PDP suka halarci taron gangamin da tsohon mataimakain shugaban kasar Najeriyar ya gudanar da nufin neman kuri'un su a zaben da za'a gudanar.

Legit.ng Hausa ta samu cewa wannan taron gangamin ne dai na farko da dan takarar ya gudanar tun bayan dawowar sa daga kasar Amurka inda yaje ziyarar kwanaki biyu tare da rakiyar shugaban yakin neman zaben nasa, Sanata Bukola Saraki.

Tun farko dai, Atiku da tawagar sa tare da rakiyar tsohon gwamnan jihar, Dakta Sule Lamido sun ziyarci Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi CON, a fadar sa.

Ga dai wasu hotunan nan:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng