Allah mai girma: Ku kalli wasu hotunan wata lokacin da yayi masassara farkon daren yau
Masu sha'awar kallon sararin samaniya sun yi ta duba sama don ganin husufin watan wanda aka fara da daren Lahadi a wasu sassan duniya kuma har daren yau Litinin a jahohin Najeriya da makwaftan ta.
A lokacin kusufin, watan na daukar launin ja sannan ya rika kyalli da haske kuma ya kan zo kusa da duniya. An fara ganin kusufin ne a Amurka da wasu bangarorin yammacin Turai.
A wasu sassan Birtaniya kuwa, giza-gizai sun lullube watan yadda ba a samu ganinsa ba.

Asali: Twitter
KU KARANTA: In dai za'a yi adalci to PDP zata ci zaben 2019 - Dogara
Ana sa rai za a yi wani kusufin watan nan da shekara biyu, ran 26 ga Mayun 2021.
"Idan iskar da ke kusa da duniya ta karkatar da hasken rana har hasken ya isa inda wata ya ke, shi ne irin wannan husufin ke aukuwa," in ji Walter Freeman, farfesa a jami'ar Syracuse da ke jihar New York.
"Wannan jan hasken da kalilan ne ke hakse wata har mu gani a nan duniya."
Irin wannan husufin watan na faruwa ne idan Doron Kasa ya shiga tsakanin Rana da Wata.
A wannan yanayin, Rana ta shiga bayan Doron Kasa ne, kuma Wata ta shiga cikin inuwar Doron Kasa.
Ga dai wasu hotunan nan kamar yadda wasu suka wallafa a shafukan su na sadarwar zamani:
Asali: Legit.ng