Obasanjo yace ya zama dole yan Najeriya su gode ma Buhari

Obasanjo yace ya zama dole yan Najeriya su gode ma Buhari

- Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ya zama dole yan Najeriya su gode ma shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasar

- Obasanjo yaba ma Buhari kan rashin kara wa’adin tsohon sufeto janar na yan sandan, Ibrahim Idris

- Ya kuma bayyana cewa wasu malamai za su riki shugaban kasar akan furucinsa game da zabe na gaskiya da amana da kuma zabe cikin zaman lafiya da lumana

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ya zama dole yan Najeriya su gode ma shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasar.

Obasanjo ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 20 ga watan Janairu a wani taron manema labarai da aka gudanar a dakin karatun Obasanjo da ke Abeokuta, babbar birnin jihar Ogun.

Legit.ng ta tattaro cewa jigon kasar yace jawabin da yayi ci gaba ne ga wasikar da ya rubutawa Buhari a watan Janairun 2018.

Ya bayyana cewa ci gaban da aka samu bayan wasikar ya tabbatar da gaskiyar abunda ke kunshe a cikinta, inda ya kara da cewa burin hasashensa ya cika.

Obasanjo yace ya zama dole yan Najeriya su gode ma Buhari
Obasanjo yace ya zama dole yan Najeriya su gode ma Buhari
Asali: UGC

Ya yaba ma Buhari kan mutunta ra’ayin yan Najeriya da suka yi kira ga nada sabon sufeto janar na yan sanda kan tsoron cewa tsohon sufeto janar na yan sandan, Ibrahim Idris, na iya taimakawa wajen yin magudin zabe.

Obasanjo wanda ya ce lallai ba za a iya share gudunmawarar da Buhari ya bayar wajen ci gaban Najeriya ba yayi adu’a cewa shugaban kasar na nan zai ga kudirin Allah akan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Obasanjo na da bukatar ganin likita - Buhari

Obasanjo ya kuma bayyana cewa wasu malamai za su riki shugaban kasar akan furucinsa game da zabe na gaskiya da amana da kuma zabe cikin zaman lafiya da lumana.

Ya kuma yi kira ga shugaban INEC da ya tsaya tsayin-daka sannan ya gudanar da aikinsa cikin kwarewa da kuma kasancewa a tsaka-tsaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng