Nasrun mina llah: Sojoji sun ragargarji yan Boko Haram a Buni Yadi (Hotuna)
A ranar Lahadi, 20 ga watan Junairu, 2018, rundunar sojin Najeriya sun sami gagarumin nasara kan mayakan Boko Haram yayinda suka kai wata mumunan hari barikin sojoji dake garin Buni-yadi, jihar Yobe.
Mataimakin kakakin rundunar 27 Brigade. Major Nureni Alimi, ya bayyana hakan ne da safiyar Litinin a shafin sadarwa hukumar sojin in da yace:
"Rundunar sojin 27 Task Force Brigade da jami'an makaran jami'an soji dake Buni Yadi, karamar hukumar Gujba na jihar Yobe, sun samu nasaran ragargazan yan Boko Haram da suka kawo hari barikin sojoji.'
"Yan ta'addan sun kawo hari barikin ne misalin karfe 4:15 na yammacin ranar Lahadi, 20 ga watan Junairu, 2018 inda sukayi artabu da soji na tsawon sa'o'i biyu da rabi. Amma Soji sun tsaya sun dakilesu."
An kwato motan bindigogi biyu kuma an hallaka wasu cikinsu inda sauran suka arce da raunuka daban-daban. Kana an kwace harsasan bindigogin baro jirage da bama-bamai."
Sojojin sun yi farin cikin inda suke murna a fili. Jami'an soji hudu kadai suka samu kananan raunuka kuma sun jinya a asibitin barikin."
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tafi jihar Borno (Bidiyo)
Kalli hotunan:

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng