Zaben 2019: Uwar gidan Atiku Abubakar ta kwancewa Buhari zane a kasuwa
Uwar gidan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Titi Atiku Abubakar ta yi kaca-kaca da shugaba Buhari da salon mulkin sa.
Hajiya Titi dai ta bayyana cewa kasar Najeriya a halin yanzu ta kasance da wata irin rarrabuwar kan da bata taba gani ba a tarihin ta sanadiyyar irin mulkin wariya da shugaban kasar yake yi yanzu.

Asali: Depositphotos
Legit.ng Hausa ta samu cewa uwar gidan ta Atiku Abubakar ta bayyana hakan ne a garin Abeokuta na jihar Ogun yayin da ta halarci wata walimar cin abinci ta girmamawa da dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP na jihar Honorabul Oladipopu Adebutu ya gayyace ta.
A don haka ne ma uwar gidan ta dan takarar ta bukaci dukkan 'yan Najeriya da su fito kwan su da kwalkwata su zabi mijin ta domin a kada Shugaba Buhari din a zaben da za'a gudanar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng