Aljanna-mai-masoya-da-yawa: An bada hutu a jihar Borno saboda zuwan Buhari

Aljanna-mai-masoya-da-yawa: An bada hutu a jihar Borno saboda zuwan Buhari

Gwamnatin jihar Borno ta sanar da ranar Litinin, 20 ga watan janairu a matsayin ranar hutu ga dukkan ma'aikatan ta saboda zuwan da shugaba Buhari zai yi jihar domin yin kamfe din tazarcen sa a tare da magoya bayan sa a ranar.

Majiyar mu ta sanar da mu cewa gwamnatin jihar ta Borno ta bayyana a cikin sanarwar bayar da hutun cewa ta yi haka ne domin ta baiwa kowa damar yin tururuwa domin zuwa tarbar shugaban kasar idan ya zo.

Aljanna-mai-masoya-da-yawa: An bada hutu a jihar Borno saboda zuwan Buhari
Aljanna-mai-masoya-da-yawa: An bada hutu a jihar Borno saboda zuwan Buhari
Asali: Twitter

KU KATANTA: Da wuya in fadi zabe - Buhari

Mai karatu dai zai iya tuna cewa ranar Litinin din nan ne dai shugaban kasar ya tsara zuwa jihohin Yobe da Borno kuma ma tuni har shirye shiren tarbar sa sun kankama a dukkan jahohin.

Shugaban kasar dai yanzu haka yana zagayawa jiha jiha ne domin gudanar da gangamin yakin neman zaben sa a zabukan da za'a gudanar kwanaki kadan masu zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng