Dogo dan Daura: Abu ne mai matukar wuya in fadi zaben 2019 - Shugaba Buhari

Dogo dan Daura: Abu ne mai matukar wuya in fadi zaben 2019 - Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce abu ne mai wahala ya fadi zaben 2019 saboda karbuwar da ya samu. Ya ce ya yi matukar gamsuwa da tarbar da ya samu a gangamin yakin neman zabensa a Bauchi da Kogi da sauran jihohin da ya ziyarta.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin da yake bayar da ansa lokacin da aka tambaye shi a wata tattaunawa da yayi ta musamman da Kadaria Ahmad kan manufofi da kudurorin sa idan ya sake zama shugaban kasa.

Dogo dan Daura: Abu ne mai matukar wuya in fadi zaben 2019 - Shugaba Buhari

Dogo dan Daura: Abu ne mai matukar wuya in fadi zaben 2019 - Shugaba Buhari
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Kotu ta bada belin Dino Melaye

An tambayi shugaban ne, idan ya fadi zabe ko zai amince da sakamakon zaben?

Ya ce ya sha faduwa zabe. "A 2003 na kare a kotu tsawon watanni 13, a 2007 na shafe wata 18 a kotu, a 2011 na share wata takwas a kotu har kotun koli."

"Sai a karo na hudu saboda ci gaban da aka samu na samar da na'urar tantance masu kada kuri'a ya kawo karshen magudin zaben da aka saba yi," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel