Da zafinsa: Shugaba Buhari ya bude babbar tashar jirgin ruwa a jihar Niger
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bude babbar tashar jirgin ruwa ta Baro, a jihar Niger
- Shugaban kasar ya samu sa hannun Rotimi Amaechi, Gwamna Sani Bello da kuma SGF, Boss Mustapha a wajen bude tashar
- Rundunar 'yan sanda ta raba dakarunta akalla 1,711 a fadin jihar domin tabbatar da tsaro har zuwa bayan kammala ziyarar shugaban kasar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da babbar tashar jirgin ruwa ta Bayo da ke jihar Niger. Tashar wacce ta lakume akalla N6bn kafin kammalata, an fara bayar da kwangilarta ne a shekarar 2011 da kuma 2012, wacce aka yi watsi da aikin, har sai a gwamnatin Buhari da ta kammala aikin.
A yammacin yau, ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da yakin zabensa a garin Minna, babban birnin jihar Niger, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito.
Tayo Fadile, babban manajan da ke kula da sashen harkokin kamfanonin kasuwanci na hukumar tashar jiragen ruwa ta kasa, ya ce tashar jirgin ruwa ta Baro ta kasance tilo a cikin Arewacin Nigeria wacce gwamnatin tarayya ta gina domin bunkasa ayyukan farfado da tekun Niger.
KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Shugaban kasa Buhari ya dira jihar Niger

Asali: Facebook
Mr Fadile, ya ce akalla tashar jirgin zuwa ta Bayo zata samar wa jama'a da guraben manyan ayyuka akalla 2,000 yayin da zata samar da kananan ayyuka ga dubunnan mutane. Haka zakilai tashar zata taimaka wajen rage yawan zirga zirgar manyan motoci a saman tituna, wanda zai kara yawan adadin rayuwar titunan.
A hannu daya kuwa, Legit.ng Hausa a baya ta ruwaito maku cewa rundunar 'yan sanda ta tura akalla jami'anta 1,711 a fadin jihar, domin tabbatar da tsaro, kafin, a lokacin da kuma bayan kammala ziyarar kwana daya da shugaban kasar ya kai jihar Niger.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng