Da dumin sa: Gwamna El-rufai yayi rashin babban yayan sa

Da dumin sa: Gwamna El-rufai yayi rashin babban yayan sa

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-rufai yayi babban rashin yayan sa kuma majibincin lamurran sa, AVM Aliyu Ahmed El-rufai mai ritaya da sanyin safiyar ranar Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa AVM Aliyu Ahmed ya rasu ne yana da shekaru 71 a duniya a wata asibin garin Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Da dumin sa: Gwamna El-rufai yayi rashin babban yayan sa
Da dumin sa: Gwamna El-rufai yayi rashin babban yayan sa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Jahohin Najeriya 13 dake da arzikin zinare

Legit.ng Hausa ta samu cewa shi dai Yayan na El-rufai ya rasu ya bar 'ya'ya shidda da mata daya kuma za'a yi jana'izar sa a masallacin Sultan Bello a gariin na Kaduna bayan sallar La'asar.

Tuni dai majiyar daga cikin iyalan mamatan ta shaida mana cewa an taho da gawar sa daga asibitin zuwa gidan sa a Kaduna domin yi masa sutura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng