Da duminsa: A yau shugaba Buhari zai halarci taron bukin mawaka da yakin zabe a Kaduna
- Bashir Ahmad, ya ce shugaban kasa Buhari zai kai ziyara jihar Kaduna a yau Juma'a, domin halartar bukin kungiyar mawaka da masu kirkira na jihar
- Haka zalika hadimin shugaban kasar ya ce Buhari zai kuma halarci taron kaddamar da yakin zabensa a babban filin wasanni na Ahmadu Bello da ke cikin Kaduna
- Mr Ahmad ya kuma ce kungiyar masu sa kai domin yakin zaben shugaban kasa Buhari a kafofin sadarwa na zamani BNMC karkashin jagorancinsa, zata kasance tare shugaban kasar
Labarin da Legit.ng ke samu daga hadimin shugaban kasa, ta fuskar kafofin sadarwa na zamani, Bashir Ahmed, na nuni da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Kaduna a yau Juma'a, domin halartar bukin kungiyar mawaka da masu kirkira na jihar.
Bashir Ahmed, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter @BashirAhmaad ya ce shugaban kasar zai kuma halarci taron kaddamar da yakin zaben shugaban kasar karkashin jam'iyyar APC a babban filin wasanni na Ahmadu Bello da ke cikin Kaduna.
Haka zalika, hadimin shugaban kasar, ya ce kungiyar masu sa kai domin yakin zaben shugaban kasa Buhari a kafofin sadarwa na zamani BNMC karkashin jagorancinsa, zata kasance tare shugaban kasar a yayin da yaje kaddamar da yakin zaben nasa da kuma halartar bukin kungiyar mawaka da masu kirkirar a Kaduna.
KARANTA WANNAN: Bayan korarsa daga APC: Okorocha ya fadi dalilin cewa al'ummar Imo su zabi Nwosu

Source: Facebook
A wani labarun kuwa, Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, a ranar Alhamis, ya ce ba zai daina goyon bayan dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar Action Alliance, AA, Uche Nwosu, na ya gaje shi saboda shi (Okorocha) ya gano "Gaskiya" a tare da Nwosu.
Rochas Okorocha ya bayyana hakan a garin Owerri, a lokacin da yake mika sabon ginin katafaren ofishin kungiyar kiristoci ta kasa, CAN, ga shugaban kungiyar na kasa, Samson Ayokunle, tare da shuwagabannin kungiyar na jihar.
Okorocha ya ce daga cikin dalilan da ya sa yake goyon bayan Nwosu, sun hada da kasancewar Nwosu mai takawa da kiyaye dokokin ubangiji.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng