Yan iska sun kai hari ga ayarin motocin dan takarar gwamnan APC a Taraba
- Wasu yan iska a Wukari, Taraba sun kai hari ga ayarin motocin dan takarar gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Taraba, Alhaji Sani Danladi
- Jakadan jumhuriyar Trinidad da Tobago, Alhaji Hassan Ardo na a wajen da aka kai hari inda aka kona motoci akalla 10
- Ba a san inda dan takarar gwamnan da wasu daga cikin aboka tafiyan nasa ba domin bayan afkuwar rikicin wasu sun tsere ciki Wukari da kuma hukumar yan sanda dake garin
Wasu yan iska a Wukari, Taraba a ranar Alhamis, 17 ga watan Janairu, sun kai hari ga ayarin motocin dan takarar gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Taraba, Alhaji Sani Danladi.
Haka zalika harda jakada jumhuriyar Trinidad da Tobago, Alhaji Hassan Ardo na a wajen da aka kai hari inda aka kona motoci akalla 10.
Legit.ng ta tattaro cewa Danladi, wanda a yanzu yake kan rangaji kamfen dinsa a yankin kudancin jihar, na a hanyarsa ta zuwa karamar hukumar Ibi lokacin da wasu matasa suka farma ayarin motocinsu a wani mararraba a Wukari.

Asali: Depositphotos
Sun yiwa mararrabar kawanya, wanda hakan ya tursasa ayari motocin rage gudu, sannan sai suka farma motocin da mutanen ciki inda aka raunata wasu da dama sannan aka sace motoci.
Ba a san inda dan takarar gwamnan da wasu daga cikin aboka tafiyan nasa ba domin bayan afkuwar rikicin wasu sun tsere ciki Wukari da kuma hukumar yan sanda dake garin.
KU KARANTA KUMA: Atiku ya zargi Buhari da yaki da yan adawa maimakon yaki da rashawa
Kakakin APC a jihar, Aaron Atimas, wanda ya kasance a wajen da abun ya faru ya zargi yan adawa da alhakin kai harin.
Kokarin da aka yi don jin bakin yan sanda a Wukari da kakakin yan sanda a Jalingo bai samu ba saboda ba a dauki wayoyinsu ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng