Buhari na shirin guje ma muhawarar yan takarar shugaban kasa - CUPP

Buhari na shirin guje ma muhawarar yan takarar shugaban kasa - CUPP

- Jam’iyyar CUPP tace tana dauke da ingantattun bayanai game da yunkurin shugaban kasa Buhari na guje ma muhawarar yan takarar shugaban kasa da zai gudana a ranar Asabar

- Kakakin jam’iyyar Imo Uochinyere ya yi wannan zargin a wata sanarwa ga manema labarai a Abuja

- Ugochinyere yace ana yunkurin ne don guje ma ci gaba da fallasa Buhari bayan rashi kokarinsa a taron da ya gudana a daren ranar Laraba

Jam’iyyun adawa a karkashin kungiyar hadin gwiwa Coalition of United Political Parties (CUPP) a ranar Alhamis, 17 ga watan Janairu tace tana dauke da ingantattun bayanai game da yunkurin shugaban kasa Muhammadu Buhari don guje ma muhawarar yan takarar shugaban kasa da zai gudaa a ranar Asabar.

Kakakin jam’iyyar Imo Uochinyere ya yi wannan zargin a wata sanarwa ga manema labarai a Abuja.

Ugochinyere yace ana yunkurin ne don guje ma ci gaba da g]fallasa Buhari bayan rashi kokarinsa a taron da ya gudana a daren ranar Laraba.

Buhari na shirin guje ma muhawarar yan takarar shugaban kasa - CUPP
Buhari na shirin guje ma muhawarar yan takarar shugaban kasa - CUPP
Asali: Depositphotos

Ugochinyere ya tuna cewa a baya CUPP ta tayar da batu akan lafiyar tunani shugabann kasar sanan ta nemi wata tawaga ta kwararru su biciki dukkanin yan takarar shugaban kasar.

Yace bayyana kokarin Buhari a wajen taron ranar Laraban a matsayi wani annoba ga kasar wanda ya mayar da yan Najeria abun dariya a idon duniya.

KU KARANTA KUMA: Cibiyar kasuwanci na Amurka ta tabbatar da ganawa da Atiku

A baya mu ji cewa Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya bayyana a jiya Laraba, 16 ga watan Janairu cewa ba zai iya amsa tambaya a kan harkallar Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ba.

Buhari ya yi wannan waskiyar ce a wani taron ganawa da shi, inda ya ce a yanzu maganar ta na a hannun kotu da majalisa, don haka magana a kan batun zai zama yi wa shari’a katsalandan.

Sannan kuma Buhari ya ce shi baida masaniya akan ko asarkala da siddabaru aka yi wa bidiyon Ganduje ko a’a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng