Cibiyar kasuwanci na Amurka ta tabbatar da ganawa da Atiku

Cibiyar kasuwanci na Amurka ta tabbatar da ganawa da Atiku

- Cibiyar kasuwaci na kasar Amurka ta tabbatar da batun yin wani ganawar sirri tare da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar

- Babbar manajar labarai da sadarwa ta cibiyar kasuwanci, Katherine Cooksey ce ta sanar da hakan

- An tattaro cewa ba za a bari masu kawo rahoto su shiga taron ba

Cibiyar kasuwaci na kasar Amurka ta tabbatar da batun yin wani ganawar sirri tare da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar,

An tabbatar da lamarin ne a wani wasika da babbar manajar labarai da sadarwa ta cibiyar kasuwanci, Katherine Cooksey ta tura wa The Cable.

Legit.ng ta tattaro cewa Cooksey, tace ba za a bari masu kawo rahoto su halarci taron ba.

Cibiyar kasuwanci na Amurka ta tabbatar da ganawa da Atiku
Cibiyar kasuwanci na Amurka ta tabbatar da ganawa da Atiku
Asali: Twitter

Ta bayyana cewa: “Mun gode da kiranmu. Taron da muke Magana akai na sirri ne, kuma babu yan jarida da za su halarta.

“Mambobin cibiyar Amurka da Afrika kadai aka gayyata. Babu masu rahoton da zai halarta.”

KU KARANTA KUMA: Karin bayani da hotuna game da zuwan Atiku Abubakar Kasar Amurka

Cibiyar kasuwancin na Amurka ya kasance azure mafi girma a kasar sannan suna kashe kudi fiye da sauran kungiyoyi a kowani shekara.

Atiku ya gina kamfen din shugabancin kasarsa kewaye da ita a kokarinsa na son habbaka tattalin arziki tare da taken 'Atiku means jobs' wato ‘Atiku na nufin ayyuka’. Sai dai ba a sai ba ko anawar zai taimaka wa kudirinsa na samar da aiki a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng