Sabon Sifeto Janar: Manyan jami'an 'yan sanda 15 da za'a tilastawa ritaya

Sabon Sifeto Janar: Manyan jami'an 'yan sanda 15 da za'a tilastawa ritaya

Akalla manyan jiga-jigan jami'an 'yan sandan Najeriya 15 ne za'a tilastawa yin ritaya daga mukaman su sakamakon nada Mohammed Adamu a matsayin sabon Sifeto Janar din 'yan sanda da shugaba Muhammadu Buhari yayi a farkon makon nan.

Kamar dai yadda muka samu, daman al'adar ma'aikata masu damara, da zarar an nada wani matsayin shugaba a wata runduna, to dukkan jami'an da suka girme shi za'a yi masu ritaya, wani lokacin ma hadda sa'annin sa.

Sabon Sifeto Janar: Manyan jami'an 'yan sanda 15 da za'a tilastawa ritaya
Sabon Sifeto Janar: Manyan jami'an 'yan sanda 15 da za'a tilastawa ritaya
Asali: Depositphotos

Legit.ng Hausa ta samu cewa shi dai Mohammed Adamu yana a matsayin mataimakin Insifecta ne wanada kuma akwai mukamin mukaddashin Sifeto janar a gaban sa amma shugaba Buhari ya tsallake su ya bashi.

Ga dai sunayen wadanda za'a yi wa ritayar dole din nan:

1. Agboola Oshodi-Glover,

2. Mohammed Katsina,

3. Sani Mohammed,

4. Peace Ibekwe-Abdallah

5. Emmanuel Inyang

6. Habila Joshak

7. Maigari Dikko

8. Usman Abubakar,

9. Usman Yakubu

10. Abdulmajid Ali,

11. Aminchi Bamaila Baraya,

12. Godwin Nwobodo,

13. Abdul Daniru Danwawu,

14. Lawal Shehu

15. Yakubu Jibrin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng