Yakin neman zabe: Cinciridon dubun dubatar magoya baya sun tarbi Buhari a Benin (Hotuna)

Yakin neman zabe: Cinciridon dubun dubatar magoya baya sun tarbi Buhari a Benin (Hotuna)

A ranar Alhamis dai ne jirgin gangamin yakin neman tazarcen Shugaba Muhammadu Buhari ya isa ganin Benin, babban birnin jihar Edo inda ya tarar da cinciridon dubun dubatar magoya baya daga sassan jihar da ma shiyyar ta kudu maso kudancin Najeriya.

Mun samu cewa dai dubban mutanen sun yi dafifi ne a filin sauka da tashin jirage na birnin na Benin ne tun da sanyin safiya suna jiran isowar shugaban kasar wanda yanzu haka yake zuwa jiha-jiha domin neman goyon bayan al'umma.

Yakin neman zabe: Cinciridon dubun dubatar magoya baya sun tarbi Buhari a Benin (Hotuna)
Yakin neman zabe: Cinciridon dubun dubatar magoya baya sun tarbi Buhari a Benin (Hotuna)
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta samu cewa da yake jawabi, shugaban kasar ya roki 'yan jihar da su zabi jam'iyyar APC daga sama har kasa a dukkan matakai domin cigaba da kwankwadar lagwadar romon demokradiyya.

Jihar Edo dai ita ce jihar shugaban jam'iyyar ta APC a mataki na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole.

Ga dai wasu daga cikin hotunan na su nan:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel