Dan takaran gwamnan APC, Sani Contact, ya tsallake rijiya da baya a garin Wukari
Jakadan Najeriya zuwa kasar Trinidad and Tobago, Hassan Ardo, da dan takaran gwamnan jihar Taraba karkashin jam'iyyar APC, Sani Danladi, ya tsallake rijiya da baya a ranan Alhamis, 17 ga watan Junairu yayinda matasan karamar hukumar Wukari suka kai musu mumunan hari.
Mun samu rahoton cewa wasu mafusatan masata wadanda ake zargin yan jam'iyyar People’s Democratic Party, PDP, sun far wa motar dan takaran yayinda suka nufi karamar hukumar Ibi na jihar Taraba.
Wani idon shaida da ya laburtawa jaridar Daily Nigerian cewa abin ya faru ne lokacin da dan takaran wanda yake yakin neman zabe a kudancin jihar ya kutsa cikin matasan yayinda suka tare shataletatalen da ke karamar hukumar Ibi.

Asali: Facebook
Tabbatar da hakan, shugaban matasan jam'iyyar APC, Habu Pari, wanda ya samu raunuka a kansa ya bayyana cewa matasan na rike da muggan makami kuma suka budewa motarsu wuta.
Game da cewarsa, matasan sun raunata mutane da dama kuma suka bankawa motoci 10 wuta kuma suka sace dukiyoyin mutanen da ke cikin motan.
Yace: "Da farko an cecemu a ofishin hukumar DSS dake nan Wukari, amma duk da hakan, a gaban ofishin suka kona motocinmu."
Sun tare hanyoyi kuma kuma kai mana hari. A yanzu haka da yamman nan, akalla mutane 15 sun jikkata sakamakon harbin bindiga."

Asali: Facebook
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng