Sabon IG ya bayyana babbar matsalar da aikin dan sanda ke fuskanta a Najeriya

Sabon IG ya bayyana babbar matsalar da aikin dan sanda ke fuskanta a Najeriya

Sabon shugaban rundunar 'yan sanda, Adamu Mohammed, ya bayyana rashin ilimin shugabanci da jagoranci bisa tsari a matsayin babban kalubale da rundunar 'yan sanda ke fuskanta a Najeriya.

Sabon shugaban rundunar 'yan sandan ya yi fadi hakan ne yayin da ya yi wata takaitaciyar bayani a wurin bikin karbar ragamar mulki daga tsohon sufetan 'yan sanda da akayi a hedkwatan rundunar da ke Abuja.

A ranar Talata ne shuagaba Muhammadu Buhari ya sanar da nadin Adamu a matsayin Sufeta Janar na 'yan sanda a wurin wani buki da akayi a Aso Rock kuma ya lika masa sabon mukamin.

Babban matsalar da ke adabar rundunar 'yan sandan - Sabon Sufeta Janar

Babban matsalar da ke adabar rundunar 'yan sandan - Sabon Sufeta Janar
Source: Original

DUBA WANNAN: Taron jin ra'ayi: Dalilin da yasa ban ce komai ba game da zargin rashawar da ake yiwa Ganduje - Buhari

Adamu ya ce rundunar 'yan sandan Najeriya tana da kwararun jami'ai da za suyi bajinta a ko ina a duniya kuma za su iya magance kallubalen tsaron da ke adabar kasar muddin akwai ingantaccen jagoranci.

IGP din ya ce zai yi amfani da kwarewarsa na aikin samar da tsaro na kasa da kasa domin maido da kimar rundunar 'yan sandan.

"Rundunar 'yan sandan Najeriya tana da kwararun jami'ai masu ilimi da kishin aikinsu kuma za su iya magance duk wani kallubale da ke fuskantar kasar nan muddin suka samu ingantaccen jagoranci.

"A cikin jami'an da ke dakin taron nan akwai kwararun da za su iya goggaya da takwarorinsu na kasashen duniya a ayyukan gida da kasa da kasa.

"Abinda kuke bukata shine shugaba da zai jagorance ku bisa tsari da zai girmama ku ya kuma kula da walwalar ku kamar karin girma da sauran abubuwa. Wannan shine abinda ake rashin sa a shugabancin rundunar 'yan sandan Najeriya," inji Adamu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel