Ranar hisabi: Kotu ta sa ranar da zata yanke hukuncin karar kwace kadarorin Uwar gidan Jonathan
Babbar kotun tarayya dake zaman ta a jihar Legas ta saka ranar 11 ga watan Fabreru a matsayin ranar da zata yanke hukunci akan karar dake gabanta ta kwace makudan kudaden da aka samu a cikin asusun ajiyar uwar gidan tsohon shugaban kasa Patience Jonathan.
Hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ce ta shigar da karar a kwanan baya inda ta bukaci kotun ta kwace kudaden daga hannun wadda suke tuhuma har sai an kammala sharia.

Asali: UGC
KU KARANTA: Maimuna Aliyu ta sake shiga sabuwar cakwakiyar kudi
Legit.ng Hausa ta samu cewa kudaden da ake tuhuma dai sun kai adadin $8,435,788.84 da kuma sama da Naira biliyan 7.35 a asusun ajiya 15 na Patience Jonathan din wanda ake kyautata zaton ta samu lokacin da ta rike mukamin Sakatariyar din din din a jihar Bayelsa.
Tun farko da Lauyan EFCC. Rotimi Oyedepo ke magana a gaban kotun, yace uwar gidan ta yi anfani ne da wata kungiya da ba ta gwamnati ba wajen karkatar da kudaden zuwa asusun ajiyar kashin kanta.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng