Jami'in hukumar Alhazai ya mayar da rarar kudin da aka ba shi har N8m

Jami'in hukumar Alhazai ya mayar da rarar kudin da aka ba shi har N8m

- Wani Jami’i na hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Niger, ya maida wa gwamnati kudin da tayi masa kari bisa kuskure

- Kudin dai ya kai kimanin naira miliyan takwas

-Jami’in yace bayan ya kammala rabon guziri ga alhazan karamar hukumar nasa sai yaga akwai rarar dala dubu 20 shine ya dawo da kudin saboda a cewarsa ba hakkinsa bane

Wani Jami’i na hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Niger, ya maida wa gwamnati tsabar kudi har dalar Amurka dubu 20 da yace anyi masa kari lokacin da aka bashi kudin guziri na Alhazan karamar hukumarsa.

Jami’in da aka mabata da suna Muhammad Salis Abubakar mai kula da karamar hukumar Rijau a hukumar alhazai na jihar, yace bayan ya rabawa Alhazan nashi kudin guzirini su 75, dalar Amurka 800 Sai yaga yana da rarar dala dubu 20 kimanin Naira Miliyan 8 na kudin Najeriya, Shine ya dawo da kudin a ofishin Hukumar Alhazan jihar saboda a cewarsa ba hakkinsa bane.

Jami'in hukumar Alhazai ya mayar da rarar kudin da aka ba shi har N8m
Jami'in hukumar Alhazai ya mayar da rarar kudin da aka ba shi har N8m
Asali: Getty Images

Hukumar Alhazan ta nuna jin dadi tare kuma da yaba wannan matakin ta kuma bashi takardar yabo ta musamman kamar yadda Daraktan Ayyuka na hukumar Malam Attahiru Bala Dukku ya tabbatar.

KU KARANTA KUMA: Buhari da Osinbajo zasu halarci taron sauraron ra’ayin yan Najeriya da zai gudana a Abuja

A halin da ake ciki kuma, hukumar Alhazan Najeriya ta kai kara a kotu domin bin kadin mutuwar wani alhajin jihar da ya fado daga saman Na’urar kai mutane saman bene ya mutu a aikin hajjin da ya gabata bisa ga bayanin mukaddashin sakataren hukumar jin Dadin Alhazan jihar Niger Umar Makun Lapai.

Yanzu dai hukumar Alhazan tace ta bude kofar biyan kudin kujerar aikin Hajji mai zuwa da za a kai Naira Miliyan daya a Banki, ta kuma gargadi maniyyata kada su ba wani jami’in hukumar kudi a hannu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng