Gaidam ya umurci asibitin Yobe da ta yi wankin koda kyauta ga yan asalin jihar

Gaidam ya umurci asibitin Yobe da ta yi wankin koda kyauta ga yan asalin jihar

- Gwamna Ibrahim Gaidam na jihar Yobe ya umurci asibitin koyarwa na jihar, Damaturu da ta yi aikin wankin koda ga marasa lafiyan da suka kasance yan asalin jihar a kyauta

- Kwaishinan harkokin cikin gida na jihar, Mala Musti ya bayyana hakan a ranar Talata

- Matsalolin gazawar koda ya yi yawa a yankunan Gashua da Nguru, lamarin da yasa gwamnan bayar da wannan umurni

Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam, ya umurci asibitin koyarwa na jihar Yobe, Damaturu da ta yi aikin wankin koda ga marasa lafiyan da suka kasance yan asalin jihar.

Kwaishinan harkokin cikin gida na jihar, Mala Musti ya bayyana hakan a ranar Talata, 15 ga watan Janairu jim kadan bayan taron yan majalisar jihar wanda gwamnan ya jagoranta a Damaturu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An tattaro cewa matsalolin gazawar koda ya yi yawa a yankunan Gashua da Nguru, lamarin da yasa gwamnan bayar da wannan umurni.

Gaidam ya umurci asibitin jiha da ta yi dashen koda kyauta ga yan asalin Yobe
Gaidam ya umurci asibitin jiha da ta yi dashen koda kyauta ga yan asalin Yobe
Asali: Depositphotos

Yace majalisar ta kuma yanke hukunci tare da amincewa das akin sama da naira biliyan hudu domin aiwatar da ayyuka daban-daban a jihar.

Daga ckin ayyukan a cewar kwamishinan sun hada da shigo da motocin Toyota Hilux 4WD guda 20 domin tallafawa tsaro akan kudi N480,000,000; gina gida mai hawa uku ga dalibai mata a jami’ar jihar Yobe akan kudi N244,355,153.05.

KU KARANTA KUMA: Shugabannin APC a Kaduna sun ba Buhari tabbacin samun kuri’u sama da kaso 90

Sauran ayyukan sun hada da gyara hanyoyi 14 a fadin yankuna uku na jihar akan N823,392,121.83; da dai sauran wasu muhimman ayyuka.

Ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da N585,516,507.78 don samar da Karin kayayyakin aiki ga asibitin koyarwa na jihar da ke Damaturu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng