Abunda na sani game da magaji na, Adamu – shugaban yan sanda mai barin gado
- A yau Talata, 15 ga watan Janairu shugaban yan sanda, Ibraim Idris ya cika shekaru 60 a duniya
- Ya mika shugabancin hukumar ga sabon IGP Adamu
- Idris ya bayar da wasu shawarwari da yake ganin za su taimaka wa sabon shugaban yan sandan wajen gudanar da aikinshi yadda ya kamata
Sufeto Janar na yan sanda mai barin gado, Ibrahim Idris, ya shawarci magajinsa da ya kewaya fadin kasar sannan ya dauki matakan da suka dace wajen inganta tsaro.
Da yake jawabi bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma agajinsa, Idris yace: “Ina son sanar da ýan Najeriya cewa a yau na cika shekar 60 a duniya sanan ina ganin na kai karshe a aikina.
“Don haka zan mika ragamar komai ga magaji na, sabon sufeto janar na yan sanda. Jami’i ne da na sani sosai. Mun san juanmu a baya, mun yi aiki tare sannan ina yi masa fatan nasara.

Asali: Facebook
“Shawarar a zan bashi kamar a lokacinmu, yayi kokai ya kewaya kasar, sannan ya dauki matakai don tabbatar da cewa rundunar yan sandan Najeriya ta bayar da isasshen kariya ga rayuka da dukiyoyi,” inji shi.
“Ina ganin zuwa yanzu a karkashin gwanatin nan, ina ganin rundunar yan sanda na ta kokari sosai wajen kare yan Najeriya. Babu shakka akwai kalubale a fannin dibar ma’aikata; tabbas kuna sane da cewa gwanati ta amince mana d diban Karin mutane a kowani shekara. Daizinin Allah, yawan yan sandan da za a diba a wannan shekarar zai karu.
KU KARANTA KUMA: Cin amana: Yan haya sun sace 'ya'yan maigida guda 2, sun sayar dasu N1m
“Tabass, muna shiryawa zabe.mun gudanar da zabuka da dama a kasar nan sannan ina ganin za ku yarda cewa rundunar yan sanda ta yi kokari a wadannan zabukan. Ina baku tabbaci cewa yan Naeriya za su yi iya bakin kokarinsu a wannan zabe mai zuwa."
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng