Cin amana: Yan haya sun sace 'ya'yan maigida guda 2, sun sayar dasu N1m

Cin amana: Yan haya sun sace 'ya'yan maigida guda 2, sun sayar dasu N1m

- Wasu yan haya sun sace 'ya'yan maigida guda biyu sannan suka siyar da kowannensu akan N500,000

- An siyar da yaran ne ga wasu mutane daga Port Harcourt a jihar Rivers da kuma Nnewi a jihar Anambra

- Zuwa yanzu dai ba a san takamaiman wurin da yaran suke ba

An siyar da yan uwan juna biyu, Christabel da Amanda wanda masu haya a gidan mahaifinsu suka sace a watan Yunin shekarar da ta gabata akan N500,000 ko wani mutum guda daga cikinsu.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa an siyar da yaran ne ga wasu mutane daga Port Harcourt a jihar Rivers da kuma Nnewi a jihar Anambra.

An sace Christabel da Amanda yan shekaru hudu da shida a kauyen Utese da ke karamar hukumar Ovia ta arewa maso yamma.

Wasu mata biyu dake haya a gidan mahaifinsu masu suna Mercy da Rose ne suka sace yaran.

Mercy da Rose sun shafe makonni uku kawa a gidan da suka yi haya lokacin da suka sace yan uwan guda biyu bayan mahaifiyarsu ta barsu a karkashin kulawarsu.

Cin amana: Yan haya sun sace 'ya'yan maigida guda 2, sun sayar dasu N1m
Cin amana: Yan haya sun sace 'ya'yan maigida guda 2, sun sayar dasu N1m
Asali: Facebook

Daya daga cikin masu laifin, wacce ta taimaka wajen sufuri da siyar da yaran, Joy Odum tayi jawabi ga manema labarai lokacin da aka gurfanar da su a jiya.

Sauran da aka gurfanar sune Ruth Ese mai shekaru 58 da Favour Uju 45.

Wata mai laifi, Esther da taimakawa Rose da Mercy wajen daukar yaran zuwa Agbor a jihar Delta na gidan yari inda take shan dauri.

Joy tace yaran sun zauna da ita na dan kankanin lokaci a Agbor kafin ta kai su wajen Ruth wacce ke a Onitsha.

Madam Ruth ta kira Favour a jihar mo wacce ta kawo ma’auratan da suka biya kudin yaran.

Ruth tace lallai har yanzu yan na raye sannan cewa aikin yan sanda ne su gano inda suke.

Tace an siyarwa wasu ma’aurata da basu da haihuwa yaran.

KU KARANTA KUMA: Hukumar INEC ta saki matakan zaben 2019 (jerin matakan)

Favour tace ita yar kasuwa ce a Owerri sannan cewa bata san inda yaran suke ba.

Tace ita dai kawai ta taimakawa ma’auratan ne wajen basu yaran da aka sato.

Mahaifin yaran, Spark Omokpia yace zai yi komai don ceto yaransa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng