Zaben 2019: Sule Lamido ya caccaki Izala da Sheik Bala Lau kan goyon baya Buhari
Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Sule Lamido, ya gargadi shugaban kungiyar Izalatul Bidia Waikamatul Sunnah JIBWIS wacce aka fi sani da kungiyar Izalah kan amfani da addini wajen raba kan yan Najeriya.
Tsohon gwamnan ya nuna bacin ransa kan rahotannin da suka bayyana cewa shugabannin kungiyar sun yi kira ga mabiyansu su zabi shugaba Muhammadu Buhari a zaben za'a gudanar nan da wata daya.
Sule Lamido, a taron yakin neman zaben PDP a garin Hadejia ya yi kira ga shugabannin Izalah da su daina hada siyasa da addini kuma su bari jama'a su zabi son ransu.
Lamido yace: "Ku nada mabiya a PDP, APC, da Apga,ku daina amfani da addini wajen raba kan yan Najeriya. Kowani dan Najeriya na da yancin zaben wanda yakeso ba tare da la'akari da addini ko akida ba."

Asali: Original
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya jagoranci taron FEC na gaggawa a yau
A baya mun kawo muku rahoton cewa kungiyar nan ta addinin Musulunci dake da dimbin mabiya a kasashen Najeriya, Kamaru, Nijar da Chadi, watau kungiyar Jama’atul Izalatil Bidi’a wa Iqamatissunnah ta bayyana Buhari matsayin gwaninta a zaben 2019.
Kungiyar ta sanar da gwanin da take ganin ya fi dacewa da mulkin Najeriya kuma ya yafi dacewa da jama’a su zaba a zaben shekarar 2019 ne ta bakin shugaban majalisar malamai ta kungiyar, Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo, inda yace Muhammadu Buhari suke so.
Assheikh Jalingo ya bayyana haka ne a yayin da yake gabatar da hudubar sallar Juma’a a wata babbar Masallaci dake garin Yola ta jahar Adamawa a ranar Juma’ar data gabata, 11 ga watan Janairun 2019, inda yayi tunatarwa akan muhimmancin zaben shugaban nagari da kuma muhimmancin shugabanci nagari.
Shehin Malamin ya gabatar da hudubar ce a ranar da shugaban kungiyar Izala, Sheikh Bala Lau ke aurar da yayansa mata guda biyu a wannan Masallaci, haka zaika shima na’ibinsa ya aurar da diya mace a bayan sallar juma’ar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng