Abun al'ajabi: An tono wata gawa da ta shekara 19 bata rube ba

Abun al'ajabi: An tono wata gawa da ta shekara 19 bata rube ba

Kamar dai yadda ta taba faruwa a cikin shekarar 1980, al'ummar garin Foko dake jihar Ibadan, ya koma kamar wata cibiya ta yawon bude ido, bayan da wata motar kwasar kasa ta tono wata tsohuwar gawa wacce aka sameta kamar yadda aka binneta shekaru masu yawa. To kusan hakan ta faru a karshen shekarar 2018, inda al'ummar Onipepeye suka wayi gari cikin mamaki da al'ajabi, bayan da aka tono gawar wani mai suna Pa Jimoh Adeniji, da aka binne shekaru 19 da sukagabata, amma har yanzu gawar bata rube ba.

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu daga jaridar Tribune ta yanar gizo, ya yi nuni da cewa al'ummar Onipepeye sun wayi gari cikin mamaki da al'ajabi, bayan da aka tono gawar wani mai suna Pa Jimoh Adeniji, da aka binne shekaru 19 da sukagabata, amma har yanzu gawar bata rube ba.

Rahotanni sun bayyana cewa Adeniji ya rasu ne a daren ranar 20 ga watan Ogusta, 1999, jim kadan bayan da ya shiga dakin kwanansa, bayan dawowarsa daga sallar Isha'i. Kamar yadda shari'ar Musulunci ta haramta binne gawa idan dare yayi, wannan yasa aka binneshi a washe garin ranar da ya rasu.

KARANTA WANNAN: Kowa yayi ya gama: Babu wanda ya isa ya hadani fada da Buhari - Amosun

Abun al'ajabi: An tono wata gawa da ta shekara 19 bata rube ba
Abun al'ajabi: An tono wata gawa da ta shekara 19 bata rube ba
Asali: Twitter

Kasancewar shugaban al'ummar, wannan yasa aka binne gawarsa a cikin hubbarensa. Sai dai bayan shekaru 19, gwamnatin jihar ta bukaci gudanar da wani aiki a garin, wanda suka bukaci rusa wasu gidaje, da ya hada da gidan da aka binne gawar Adeniji a ciki. Wannan dalilin ne kuma ya sanya iyalansa suka bukaci a tono gawarsa, koda kuwa kasusuwansa ne, domin sauya masu makwanci.

A cewar daya daga cikin matan mamacin, Alhaja Misitura Adeniji, an kirawo wadanda zasu hako ramin, inda suka fara aiki gadan-gadan. Sai dai aikin ya dan dau lokaci kasancewar kasar wajen tayi tauri. A yayin da suka yi nisa da ginin, sai suka rinka jiyo kamshin turare, wanda ya kara karfi a lokacin da suka riski itatuwan da aka rufe ramin.

"Bayan cire itatuwan, sai gaba daya muka cika da al'ajabi da mamakin abubuwan da idanuwanmu suka gani. Gawar tana nan cikin likafaninta kamar yadda aka binneta shekaru 19 da suka gabata, babu wata alama ta rubewa a jikin likafin ko jikin gawar. Wannan yasa muka fara kiran sunan Allah da "Allahu Akbar."

Matar ta bayyana mijinta a matsayin mutum wanda ya ke da takawa, da taka tsantsan wajen bin dokokin addinin Musulunci, haka zalika baya wasa da ibadunsa. Ta kuma shawarci jama'a da su kasance masu jin tsoron Allah a rayuwarsu don samun kyakkyawar makoma a ranar gobe kiyama.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng