Rigar kowa: Mutuwa ta dauke jiga-jigan jam'iyyar PDP 2 a jihar Arewa

Rigar kowa: Mutuwa ta dauke jiga-jigan jam'iyyar PDP 2 a jihar Arewa

Akalla shugabannin jam'iyyar adawa ta People’s Democratic Party (PDP) a karamar hukumar Shendam na matakin mazaba suka rasa rayukan su a kan hanyar su ta komawa gida bayan kammala taron gangami da dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar, Atiku Abubakar ya gudanar.

Kamar yadda muka samu, mutanen sun mutu ne lokacin da motar da suke ciki ta rabu da hanya ta kuma kutsa cikin daji inda nan take suka ce ga garin ku nan yayin da kuma sauran cikin motar suka samu raunuka.

Rigar kowa: Mutuwa ta dauke jiga-jigan jam'iyyar PDP 2 a jihar Arewa
Rigar kowa: Mutuwa ta dauke jiga-jigan jam'iyyar PDP 2 a jihar Arewa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Atiku ya rasa magoya baya 800,000

Legit.ng Hausa ta samu cewa tuni dai dan takarar shugabancin kasar Atiku Abubakar ya jajantawa iyalan mamatan da hatsarin ya rutsa da su sannan yayi alkawarin taimaka masu.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a cikin karshen makon nan ne dan takarar shugabancin kasar a jam'iyyar PDP ya gudanar da gangamin neman zaben sa a garin Jos, babban birnin jihar Filato dake shiyyar Arewa ta tsakiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel