Zaben 2019: Abunda za mu yiwa Atiku Abubakar idan yazo Kano - Maryam Gawuna

Zaben 2019: Abunda za mu yiwa Atiku Abubakar idan yazo Kano - Maryam Gawuna

Kamar yadda kungiyoyin dake kasar nan ke yi wa dan takarar shugaban kasar nan a tutar jam’iyyar PDP Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar tarba a duk jihohin da yan je yakin neman zabe.

Mu ma magoya bayan jam’iyyar PDP musamman masu kaunar ganin Atiku ya zama shugaban kasa 2019 mun shirya gagarumar tarba gareshi a jihar Kano musamman ranar da zai shigo jihar yakin neman zaben shugaban kasa da yardar Allah.

Zaben 2019: Abunda za mu yiwa Atiku Abubakar idan yazo Kano - Maryam Gawuna
Zaben 2019: Abunda za mu yiwa Atiku Abubakar idan yazo Kano - Maryam Gawuna
Asali: Facebook

KU KARANTA: Wata mata ta auri kan ta a Afrika

Wannan bayani ya fito ne daga bakin shugabar mata ga kungiyar ‘Bata Global Phone Assoceries Sellers for Mobement Associations 2019’ dake Kano, Hajiya Maryam Musa Gawuna, a lokacin da take zantawa da manema labarai a Kano.

Hajiya Maryam Musa Gawuna ta ce an kafa kungiyar ne domin taimakawa Atiku ya samu nasaran lashe shugabancin kasar nan 2019, domin tsohon mataimakin shugaban kasar yake da tsare tsare masu kyau domin ci gaban ‘yan kasuwa da kuma kungiyoyi.

A cewar ta, wannan ne ya sa kungiyar tasu da suka kafa ta dukufa wajen tallata manufofin ta a wasu kasuwannin dake jihar domin taimakawa dan takarar na su na PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng