Yanzu-Yanzu: Kotu ta amince a cigaba da shari'ar cafko matar Ganduje

Yanzu-Yanzu: Kotu ta amince a cigaba da shari'ar cafko matar Ganduje

Wata babbar kotun tarayya dake zaman ta a garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ta amince a cigaba da shari'ar dake gabanta da ka iya sa a tilastawa hukumar EFCC kama uwar gidan Gwamnan Kano, Hajiya Hafsatu Abdullahi Ganduja bisa zargin tafka almundahana.

Kamar dai yadda muka samu, shari'ar da aka shigar gaban kotun tana tuhumar uwar gidan Gwamnan Kano din ne da hannu damu dumu tare da wasu tsiraru wajen yin almundahana da dukiyar 'yan Kano da ake zargin mijin ta da yi.

Yanzu-Yanzu: Kotu ta amince a cigaba da shari'ar cafko matar Ganduje
Yanzu-Yanzu: Kotu ta amince a cigaba da shari'ar cafko matar Ganduje
Asali: Facebook

KU KARANTA: EFCC tayi karin haske game da tura Ibrahim Magu karatu

Legit.ng Hausa ta samu cewa da kotun ke yanke hukunce game da karar, ta umurci hukumar ta EFCC da ta hanzarta bincikar wadanda ake tuhuma a karar da aka shigar.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya gidan jaridar Daily Nigerian ta wallafa wasu fayafayan bidiyoyi dauke da gwamnan na Kano yana karbar cin hanci da rashawa a ofishin sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel