Yanzu Yanzu: Atiku ya shiga alhini yayinda masoyansa suka mutu a hatsarin mota, ya ba da umurni akan wadanda suka jikkata

Yanzu Yanzu: Atiku ya shiga alhini yayinda masoyansa suka mutu a hatsarin mota, ya ba da umurni akan wadanda suka jikkata

Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar a ranar Lahadi, 13 ga watan Janairu ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota a hanyarsu ta zuwa gida daga gangamin jam’iyyar a jihar Plateau a ranar Asabar, 12 ga watan Janairu.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar mika sakon gaisuwa da alhini ga iyalan magoya bayarnsa da suka mutu yayin komawa gida daga wajen kamfen dinsa a jihar Plateau.

Atiku ya kuma bayar da umurnin cewa a bayar da cikakken taimako ga wadanda suka tsira daga hatsarin sannan suke kwance a asibiti a yanzu haka.

Yanzu Yanzu: Atiku ya shiga alhini yayinda masoyansa suka mutu a hatsarin mota, ya ba da umurni akan wadanda suka jikkata
Yanzu Yanzu: Atiku ya shiga alhini yayinda masoyansa suka mutu a hatsarin mota, ya ba da umurni akan wadanda suka jikkata
Asali: Twitter

A wani jawabi dauke da sa hannun Paul Ibe, kakakin tsohon mataimakin shugaban kasar, ya bayyana Christy Yelick Dungtou da Donatus Morkwap a matsayin wadanda suka mutu.

Sun kasance mambobin daya daga cikin kungiyyin goyon bayan PDP sannan suna a hanyarsu ta zuwa Shendam bayan gangamin Jos.

KU KARANTA KUMA: Goyon bayan Buhari da kake yi ya saba ma ra’ayin yan Igbo – Atiku ga Obiano

“Kwalmi Julius, daya daga cikin wadanda suka samu rauni da ke cikin mawuyacin hali na samun kulawar likitoci a asibitin Plateau, Jos yayinda sauran biyun aka mayar da su Shendam,” cewar sanarwar.

Ya kara da cewa kungiyar kamfen din Atiku Abubakar ta hade da wani jami’in kungiyar wanda ya tabbatar da cewa an mika gawawwakin wadanda suka mutun zuwa daki ajiye gawa a karamar hukumar Shendam da ke jihar Plateau.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel