An gudanar da jana'izar Sarkin Lafiya, Isa Agwai

An gudanar da jana'izar Sarkin Lafiya, Isa Agwai

- An yi jana'izar Sarkin Lafiya, Marigayi Isa AlMustapha Agwai cikin fadarsa a yau Juma'a

- Marigayi ya rasu ya bar 'ya'ya biyu; Alhaji Musa Isa AlMustapha Agwai da kuma Hajiya Hauwa Isa Mustapha Agwai

- Babban Limanin jihar Nasarawa, Malam Dalhatu Muhammad Dahiru, shine ya jagoranci sallar a yammacin yau na Juma'a

A yau Juma'a, an gudanar da jana'izar sarkin Lafiya, Marigayi Isa AlMustapha Agwai I, cikin fadarsa ta garin Lafiya da ke jihar Nasarawa yayin da hawaye suka kwaranya tare da jimamin wannan babban rashi na kasar Najeriya baki daya.

An gudanar da jana'izar Sarkin garin Lafiya na 16 cikin fadarsa da ya riga mu gidan gaskiya a jiya Alhamis bayan wata 'yar gajeruwar rashin lafiya da ta zamto ma sa sanadiyar ajali.

Babban Limamin garin Lafiya, Malam Dalhatu Muhammad Dahiru, shine ya jagoranci sallar jana'izar da misalin karfe 3.15 na yammacin yau Juma'a tare da 'yan uwa, makusanta da abokanan arziki.

An gudanar da jana'izar Sarkin Lafiya, Isa Agwai

An gudanar da jana'izar Sarkin Lafiya, Isa Agwai
Source: UGC

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, ajali ya katse hanzarin Marigayi Isa Agwai a wani asibitin koyarwa na kasar Turkiya da ke garin Abuja bayan ya shafe shekaru arba'in da uku a bisa karagar mulki ta masarautar birnin Lafiya da kasance masaurautar jihar Nasarawa baki daya.

Jiga-jigai da suka halarci jana'izar dattijon da ya shekara 84 a duniya sun hadar da gwamnan jihar Nasarawa; Tanko Al-Makura, Sultan na Sakkwato; Sa'ad Abubakar III, Sanata Abdullahi Adamu, Ministan ruwa; Sulaiman Adamu da kuma sarakunanan gargajiya daga sassa daban-daban na kasa.

KARANTA KUMA: Wa'adi: Ababe 5 da ya kamata ku sani game da Marigayi Sarkin Lafiya

Ya rasu ya bar 'ya'ya biyu; Alhaji Musa Isa AlMustapha Agwai da kuma Hajiya Hauwa Isa Mustapha Agwai. An kuma binne shi gidan su na gado na Marigayi Mamman Ari Agwai da ke kofar Kaura a garin Lafiya.

Tarihi ya bayyana cewa, an haifi Marigayi Isa Agwai a shekarar 1935 a kofar Kofar da ke garin Lafiya da ya kasance da ga Muhammad Al-Mustapha Marafa da kuma Mahaifiyar sa; Hajiya Halimatu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel