Zaben 2019: INEC ta bayyana hanyoyi 7 da masu zabe zasu bi wajen kada kuri'arsu

Zaben 2019: INEC ta bayyana hanyoyi 7 da masu zabe zasu bi wajen kada kuri'arsu

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta bbayyana wasu hanyoyi da masu zabe zasu bi a yayin da suka je kad'a kuri'arsu, a baban zaben 2019. Hukumar ta bayyana hakan a shafinta na Twitter @inecnigeria.

Duba hanyoyi bakwai da ya kamata masu zabe su bi a yayin kad'a kuri'aru, kamar yadda INEC ta zayyana.

Mataki na 1:

A yayinda ka isa akwatin kad'a kuri'arka, ka bi sahun layin da ka taras, kana ka gabatar da kanka gaban jami'in INEC (APO111) a rumfar akwatin zaben wanda shine zai duba bayananka don sanar da kai ko lallai nan ne rumfar zabenka, kuma zai tabbatar da cewa hoto da lambar katin zabenka (PVC) sunyi dai-dai da fuskarka. Idan komai ya tafi dai-dai, jami'in zai sanyaka a hanya don haduwa da jami'i na gaba (APO1).

Mataki na 2:

Jami'in INEC na gaba (APO1) zai bukaci ka nuna masa katin zabenka don tabbatar da cewa katin ba jabu bane, zai yi hakan ta hanyar sanya katin a cikin na'urar tantance katin masu kada kuri'a. Jami'in zai bukaci ka dora d'an yatsanka akan na'urar wacce zata nuna cewa katin da ka gabatar naka ne, na'urar zata fitar da suna, hoto da kuma sachin yatsun duk wadanda zasu kada kuri'a a zaben.

KARANTA WANNAN: Duba matakan da zaka bi domin yin rejistar 2019 UTME - JAMB

Zaben 2019: INEC ta bayyana hanyoyi 7 da masu zabe zasu bi wajen kada kuri'arsu

Zaben 2019: INEC ta bayyana hanyoyi 7 da masu zabe zasu bi wajen kada kuri'arsu
Source: Depositphotos

Mataki na 3:

Daga nan zaka hadu da jami'i na gaba (APO11) wanda zai bukaci ka nuna masa katin zabenka, domin dubawa ko kana cikin jadawalin masu kad'a zabe a cikin kundin masu zabe na akwatin. Zai sa alama a gaban sunanka, tare da mayar maka da katin zabenka. Jami'in zai sanya alamar tawada a yatsanka don nuna cewa an tantanceka. (Idan har ba a samu sunanka a kundin ba, ba za a barka kayi zabe ba.)

Mataki na 4:

Jami'in da ke kula da akwatin (PO) zai buga hatimi, ya sa hannu da kuma kwanan wata a takardar kad'a kuri'a. Jami'in zai juyar da takardar zaben gaba zuwa baya a lokacin da zai baka. Jami'in zai sanyaka a hanyar da zaka kad'a zaben naka, cikin sirri.

Mataki na 5:

Zaka yi amfani da yatsan da ya dace wajen dangwala kuri'arka bayan ka sanyawa yatsan tawadar da zata makale jikin jam'iyya/dan takarar da kake muradin zaba. Bayan ka kammala hakan, sai ka nade takardar kamar yadda jami'i (PO) ya baka tun farko.

Mataki na 6:

Daga nan sai ka bar bangaren dangwala kuri'ar taka tare da jefa takardar cikin akwatin jefa kuri'u da aka tanadar wanda kuma yake a bainar jama'a.

Mataki na 7:

Daga nan ne zaka bar rumfar zaben ko kuma ka jira daga nesa cikin nutsuwa ba tare da tayar da hatsaniya ba, har zuwa lokacin da za a kammala kad'a kuri'ar tare da kidaya sakamako.

KA KULA: Bayan kammala kad'a kuri'un kowa, za a sanar da sakamakon zaben wannan akwati a gaban kowa, domin zama shaida.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel