Yanzu-yanzu: Tsohon shugaba PDP, Adamu Muazu ya koma APC

Yanzu-yanzu: Tsohon shugaba PDP, Adamu Muazu ya koma APC

Rahoton da ke shigo mana da dumi-dumi na nuna cewa tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP kuma tsohon gwamnan jihar Bauchi, Ahmed Adamu Muazu, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress APC.

Daya daga cikin masu kare muradun shugaba Muhammadu Buhari a kafofin ra'ayi da sada Zumunta, Kayode Ogundamisi, ya bayyana hakan ne da yammacin nan inda yace: "Tsohon shugaban PDP, Alhaji Adamu Muazu, ya ajiye yakin neman zaben Atiku, ya koma APC"

A bangare guda, Tsohon shugaban matasa na babbar jam’iyyar adawa Peoples Democratic Party (PDP) a mazabar Nuku-Sabon Gari da ke yankin Abaji, Mista Peter Yanzu, da wasu mambobin jam’iyyar 157 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Tsohon shugaban matasan yayinda yake jawabi a madadin masu sauya shekar a ranar Laraba a makarantar firamare na Nuku, cewa shi da sauran mambobin suna PDP tun a 1999 amma daga bisani sai jam’iyyar da suka yiwa aiki ta yasar da su.

Yace tun da jam’iyyar ta yasar da su, sun yanke shawarar yasar dasu, sun yanke hukuncin komawa jam’iyyar APC bayan yawan tattaunawa da wasu tsoffin mambobin PDP a yankin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel