Zan ba mata da matasa ayyukan yi idan na zama shugaban kasa - Atiku

Zan ba mata da matasa ayyukan yi idan na zama shugaban kasa - Atiku

- Atiku Abubakar ya jadadda alkawarinsa na samar da ayyukan yi da dama ga mata da matasan da basu da aikin yi a fadin kasar idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa

- Dan takarar shugaban kasar yayi kirarin cewa sama da yan Najeriya miliyan 10 ciki harda mata da matasa ne suka rasa ayyukansu a sekaru uku da rabi da jam’iyyar APC ta yi a mulki

- Yace gwamnatin APC ta gaza cika alkawaran zaben da ta dauka a 2015 na yaki da rashawa, rashin tsaro da kuma tarin talauci a fadin Najeriya

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, ya jadadda alkawarinsa na samar da ayyukan yi da dama ga mata da matasan da basu da aikin yi a fadin kasar idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Ya jadadda alkawarin nasa a ranar Laraba, 9 ga watan Janairu a Minna, yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a wani gangami inda ya kuma baje koli akan bukatar yin ayyukan ci gaba a jihar Niger.

Zan ba mata da matasa ayyukan yi idan na zama shugaban kasa - Atiku

Zan ba mata da matasa ayyukan yi idan na zama shugaban kasa - Atiku
Source: Twitter

Dan takarar shugaban kasar yayi kirarin cewa sama da yan Najeriya miliyan 10 ciki harda mata da matasa ne suka rasa ayyukansu a sekaru uku da rabi da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tayi a kasar.

Atiku yayi alkawarin samar da dama da ayyuka yi a kasar baki daya.

KU KARANTA KUMA: Sanata Shehu Sani ya zargi uwargidan Gwamna El-Rufai da kalaman kiyayya

Ya bayyana cewa ayyukan ci gaba da akayi a kasar da suka hada da makarantu, hanyoyi da asibitoci duk gwamnatin baya ta PDP ce tayi inda yayi kira ga yan Najeriya da suyi waje da jam’iyya mai mulki.

A cewarsa, gwamnatin APC ta gaza cika alkawaran zaben da ta dauka a 2015 na yaki da rashawa, rashin tsaro da kuma tarin talauci a fadin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel