Daga PDP har Atiku sun san cewa Buhari mai gaskiya ne – Osinbajo

Daga PDP har Atiku sun san cewa Buhari mai gaskiya ne – Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yami Osinbajo ya bayyana cewa PDP da dan takarar su na shugaban kasa, Atiku Abubakar sun san cewa Buhari mutun ne mai gaskiya

- Osinbajo ya bayyana cewa indai da Buhari toh arzikin Najeriya na hannun tsira

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yami Osinbajo ya bayyana cewa mambobin jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) dad an takarar su na shugaban kasa, Alhai Atiku Abubakar sun san cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari mutun ne mai gaskiya.

Osinbajo ya bayyana hakan yayinda yake jawabi a gangamin `Drive 4 Buhari-Osinbajo’ wanda kungiyar kamfen tare da sauran kungiyoyin magoya bayan APC suka shirya a yau Talata, 8 ga watan Janairu a Abuja.

Daga PDP har Atiku sun san cewa Buhari mai gaskiya ne – Osinbajo

Daga PDP har Atiku sun san cewa Buhari mai gaskiya ne – Osinbajo
Source: UGC

Da yake tuni ga wani furucin Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, Osinbajo ya bayyana cewa indai da Buhari toh arzikin Najeriya na hannun tsira.

Da farko da yake amsa wani tambaya kan a wani banki za su yarda su ajiye kudinsu, Bankin Atiku ko Bankin Buhari Bello yace:

“Ba zan yi Magana da yawa ba, zan baku wasu yan misalai daga nan sai ku zabi ra’ayinku. Saboda a bayyane yake bambamcin APC da kowani jam’iyyun siyasa.

“Duk inda kuka je, ku nemi amsar wata tambaya mai sauki – akwai bankuna biyu, daya shine Bankin Buhari, dayan kuma shine bankin Atiku, a ina za ku zuba kudadenku?"

KU KARANTA KUMA: Na yiwa yan Igbo adalci duk da karancin kuri’unsu gare ni – Buhari

Sai aka fashe da dariya. Ana ta ihun Bankin Buhari.

“Talakawa sun san cewa kudinsu na hannun tsira a bankin Buhari; ko Atiku ya san cewa kudinsa na hannun tsira a bankin Buhari,” inji Bello.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel