Yanzu-Yanzu: An sako 'yan agajin da aka sace a kan hanyar Sokoto

Yanzu-Yanzu: An sako 'yan agajin da aka sace a kan hanyar Sokoto

Labarin da muke samu da dumi-dumin sa yanzu haka shine na cewa 'yan bindigar da suka yi garkuwa da 'yan agajin nan su kusan 20 a kan hanyar su ta zuwa Sokoto wadanda suke dawowa daga taron atisayi da suka gabatar a jihar Kebbi karkashin kungiyar Izalar Jos.

Duk dai dai bamu samu labarin ainihin ko an biya kudin fansar su ko kuwa haka nan aka sako su. Wata majiyar ta tabbatar mana da cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi a basu kudin fansa Naira miliyan talatin (N30m).

Yanzu-Yanzu: An sako 'yan agajin da aka sace a kan hanyar Sokoto
Yanzu-Yanzu: An sako 'yan agajin da aka sace a kan hanyar Sokoto
Asali: Facebook

KU KARANTA: Wani katon asara ya rufe uwar sa da duka har ta mutu

Mai karatu dai zai iya tuna cewa ranar lahadin sati biyu da suka gabata ne masu garkuwa da mutane sukayi awun gaba da 'yan Agaji 20 wadanda suke dawowa daga taron atisayi da suka gabatar a jihar Kebbi karkashin kungiyar Izalar Jos.

'Yan Agajin dai guda ashirin sun gamu da masu garkuwa da mutanen ne a kan hanyar su ta dawowa daga jihar Kebbi, inda suka gudanar da taron atisaye (camping) wanda majalisar agaji ta kasa ta kungiyar ta shirya.

Amma kamar yadda muka samu, da suka doshi dajin Gurbin Baure dake hanyan Jibiya ta jihar Katsina sai suka ci karo da masu garkuwa da mutane. 'Yan ggajin dai su kimanin 20 dukkanin su 'yan karamar hukumar Isa ne na jihar Sokoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel