Hare haren Boko Haram: Kar ku bar gidajenku - Gaidam ya shawarci al'umar Yobe

Hare haren Boko Haram: Kar ku bar gidajenku - Gaidam ya shawarci al'umar Yobe

- Gwamna Ibrahim Gaidam na jihar Yobe, ya yi kira ga al'ummar garuruwan da ta'addancin mayakan Boko Haram ya shafa, da su hakura su zauna a gidajensu

- Ya ce kiran ya zama wajibi ne, sakamakon wani rahoto na cewar wasu mazauna garuruwan da hare haren ya shafa suna yin hijira daga matsugunnansu zuwa cikin birane

- Gaidam ya ce hukumomin tsaro na matukar kokari wajen ganin sun tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar

Gwamna Ibrahim Gaidam na jihar Yobe, ya yi kira ga al'ummar garuruwan da ta'addancin mayakan Boko Haram ya shafa, da su hakura su zauna a gidajensu, yana mai basu tabbacin kariya da kuma tsaro, ma damar basu bar gidajen nasu ba.

A cikin wata sanarwa daga daraktan watsa labaransa, Abdullahi Bego, wacce aka rabawa manema labarai, Gaidam ya ce hukumomin tsaro na matukar kokari wajen ganin sun tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al'ummar da hare haren Boko Haram din ya shafa.

KARANTA WANNAN: Karshen duniya: An hasko bidiyon wani malami na lalata da 'yar shekaru 5 ta dubura

Hare haren Boko Haram: Kar ku bar gidajenku - Gaidam ya shawarci al'umar Yobe
Hare haren Boko Haram: Kar ku bar gidajenku - Gaidam ya shawarci al'umar Yobe
Asali: Depositphotos

A cewar sanarwar, Gwamna Ibrahim Gaidam ya damu matuka ga halin da jihar ta tsinci kanta a ciki, musamman ma al'ummar garin Kukareta, Buni-Gari da Katarko, wadanda ke barin muhallanci saboda tsoron hare haren 'yan ta'addan, duk da cewar shima yana nuna damuwarsa a fili kan halin da suke ciki.

Ya ce biyo bayan hare haren da Boko Haram ta kai garuruwan Kuka Reta, Katarko da Buni-Gari da ke jihar, gwamnatin Yobe na kiran al'umar jihar da su ci gaba da hakuri tare da zaunawa a cikin gidajensu, sakamakon kokarin jami'an tsaro na tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da kuma kare rayuka da dukiyoyinsu.

Ya ce kiran ya zama wajibi ne, sakamakon wani rahoto da ke yawo na cewar wasu mazauna garuruwan da hare haren ya shafa suna yin hijira daga matsugunnansu zuwa cikin birane.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel