Maza na neman lalata da ni saboda na fito takara - Inji wata 'yar siyasa a Najeriya

Maza na neman lalata da ni saboda na fito takara - Inji wata 'yar siyasa a Najeriya

Wata 'yar siyasa da ta fito takarar a wata jam'iyyar adawa ta Mass Action Joint Alliance (MAJA) a jihar Edo mai suna Charity Idahosa ta koka akan yadda tace abokan siyasar ta na cin zarafin ta ta hanyar neman yin lalata da ita duk kuwa da ba ta son hakan.

Charity Idahosa wadda take takarar kujerar 'yar majalisar jihar a mazabar karamar hukumar Oredo ta Yamma ta bayyana cewa tana fuskantar matsalat ne a wajen yakin neman zaben ta da kuma neman goyon bayan 'yan siyasar.

Maza na neman lalata da ni saboda na fito takara - Inji wata 'yar siyasa a Najeriya

Maza na neman lalata da ni saboda na fito takara - Inji wata 'yar siyasa a Najeriya
Source: Original

KU KARANTA: Jami'an tsaron Najeriya sun yi wa 'yan ta'adda mummunar barna

Legit.ng Hausa ta samu cewa Charity Idahosa ta bayyana hakan ne a lokacin da take zantawa da manema labarai a garin Benin, babban birnin jihar ta Edo kuma da aka nemi ta bayyana sunayen masu neman ta da lalatar sai ta ki fadar sunayen su.

A wani labarin kuma, wani dan majalisar wakilan Najeriya dake wakiltar mazabar Ibeju-Lekki mai suna Hon Kabiru Abayomi Ayeola da ya rasu bayan 'yar gajeruwar rashin lafiya a wata asibiti dake a garin Legas.

Kamar dai yadda muka samu, dan majalisar ya rasu ne da yammacin ranar Lahadi 30 ga watan Disemba.

Shi dai Hon Kabiru Abayomi Ayeola kafin rasuwar sa yana wakiltar mazabar sa ne kuma dan jam'iyyar APC ne kuma ya rasu ne yana da shekaru 60 a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel