Rashin tabbas da tashin hankali ya mamaye hukumar yan sandan yayinda wa'adin IGP Ibrahim Idris zai kare yau

Rashin tabbas da tashin hankali ya mamaye hukumar yan sandan yayinda wa'adin IGP Ibrahim Idris zai kare yau

Tashin hankali da rashin tabbas ya mamaye hukumar yan sandan Najeriya kan abinda zai faru a gidan hukumar yayinda wa'adin babban sifeto janar na yan sanda, Ibrahim Kpotum Idrs, zai kare cikin sa'o'i 24.

IGP Ibrahim Idris ne shugaban hukumar yan sanda na 19 a tarihin hukumar, wanda shugaba Muhammadu Buhari ya nada ranan 21 ga watan Maris, 2016 domin maye tsohon IG, Solomon Arase.

Ya shiga hukumar yan sandan Najeriya ne a shekarar 1984 kuma ya cika shekaru 34 da aiki a wannan hukuma.

Rashin tabbas da tashin hankali ya mamaye hukumar yan sandan yayinda wa'adin IGP Ibrahim Idris zai kare yau
Rashin tabbas da tashin hankali ya mamaye hukumar yan sandan yayinda wa'adin IGP Ibrahim Idris zai kare yau
Asali: Depositphotos

Sifeton wanda haifaffen jihar Neja ne zai cika shekaru 60 kuma bisa ga dokan hukumar, za'a yiwa duk wanda ya kai shekaru 60 ritaya. Amma an samu rahotannin cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na shirin kara masa wa'adi har bayan zaben 2019.

Saboda haka, korafe-korafe da maganganu sun fara kwarara daga kungiyar fafutuka da jam'iyyar PDP kan cewa kada shugaba Buhari ya sake ya karawa IGP Ibrahim Idris wa'adi, kawai ya nada wani sabon IGP.

KU KARANTA: Boko Haram: Jirgin yakin rundunar sojin sama ya bace a Borno

Daya daga cikin wadannan kungiyoyi mai suna, Network on Police Reform in Nigeria, NOPRIN, ta yi kira ga shugaba Buhari kada ya kara wa'adin IGP Idris da sauran manyan hafsoshin hukumar sojin Najeriya.

Shugaban kungiyar NOPRIN, Mr. Okechukwu Nwaguma, ya saki jawabi inda ya kalubalanci shugaba Muhammadu Buhari kan alkawarin da yayi a sakon sabuwar shekararsa cewa zai tabbatar da zaben lumana a 2019.

Idan har yanada niyya cika wannan alkawari kada ya karawa sifeto janar na hukumar yan sandan wa'adi bayan karewar wa'adinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel