Boko Haram: Har yanzu babu duriyar 'yan sanda 40 da aka tura Baga

Boko Haram: Har yanzu babu duriyar 'yan sanda 40 da aka tura Baga

Har yanzu babu wani labari game da 'yan sandan sintiri da aka tura garin Baga, a lokacin da garin yake tsaka da rikicin 'yan ta'adda, watannin baya kadan, kafin ranar Laraba, inda tsagin mayakan Boko Haram karkashin shugabancin Albarnawi suka kai mummunan farmaki a garin.

Haka zalika, akwai yiyuwar yan sanda 13 sun yi bagan dabo a wannan bata kashin, sakamakon rashin jin duriyarsu tun bayan faruwar lamarin a yammacin ranar Laraba, lokacin da shugaban Boko Haram Habib da tsagin tawagarsa suka kai farmaki a kauyen da nufin kwace shi tare da kafa tutarsu.

Wata majiya mai tushe daga shelkwatar rundunar 'yan sanda, da ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce: "Har yanzu babu wani labari dangane da yan sandan sinitiri 40 da yan sandan cikin gida 13 da aka turasu garin Baga, jihar Borno, tun bayan harin da aka kaiwa garin a ranar Laraba."

KARANTA WANNAN: Boko Haram: Jirgin yakin rundunar sojin sama ya bace a Borno

Boko Haram: Har yanzu babu duriyar 'yan sanda 40 da aka tura Baga

Boko Haram: Har yanzu babu duriyar 'yan sanda 40 da aka tura Baga
Source: Depositphotos

"Sai dai da ikon Allah, muna fatan cewa zasu dawo garemu cikin koshin lafiya. Bari na baku tabbacin cewa da irin horon da suka samu, ina da yakinin zasu iya jurewa kuma su fafata, idan kuma ta kama na su janye, to suna da dabarun yin hakan har sai sun jira isowar agaji daga rundunar soji kafin su dawo garemu.

"Tabbas munji cewa akwai wadanda harin ya rutsa da su amma ba zamu iya sanin ko harin ya lakume rayukan mutanenmu ko bai yi ba, saboda har yanzu bamuji wata duriyarsu ba tun bayan faruwar harin."

Kakakin rundunar soji Birgediya Janar Sani Usman, a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Alhamis, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ana ci gaba da fatattakar yan ta'addan wadanda suka zo da shirin kisa da kuma sacewa ko lalata duk wasu kayan gwamnati da ke a garin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel