Da duminsa: An damke wadanda suka sace yan biyun jihar Zamfara (Kalli Hotuna da jerin sunayensu)

Da duminsa: An damke wadanda suka sace yan biyun jihar Zamfara (Kalli Hotuna da jerin sunayensu)

Jami'an hukumar yan sandan Najeriya sun damke wasu yan fashi da garkuwa da mutane da suka addabi jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya. Wadannan yan ta'addan ne suka sace wasu yan mata yan biyu kwanakin baya.

Babban jami'in hukumar yan sanda, DCP Abba Kyari ya bayyana hakan ne a ranan Litinin, 31 ga watan Disamba, 2018 a shafinsa ta Facebook inda ya jero sunayensu:

Da duminsa: An damke wadanda suka sace yan biyun jihar Zamfara (Kalli Hotuna da jerin sunayensu)
Da duminsa: An damke wadanda suka sace yan biyun jihar Zamfara (Kalli Hotuna da jerin sunayensu)
Asali: Facebook

i. Nafiu Usman 28yrs a.k.a Baba Doctor,

ii. Ma'aruf Usman daga Wanari a Zurmi

iii. Inusa Usman 40yrs daga Zurmi

iv. Awal Jibril 41yrs daga Mada LGA

v. Shehu Mohammed 55yrs

vi. Alhaji Ibrahim Ibrahim 35yrs

vii. Ibrahim Sani 45yrs

viii. Kabiru Usman 30yrs

ix. Bala Garba 60yrs

x. Maigari Labbo 56yrs

xi. Mohammed Abdullahi Aramako 31yrs

xii. Salisu Mamman Wadatau 38yrs daga Danjibga

KU KARANTA: Zamu iya kawar da ta'addanci a 2019 - Atiku

Idan za’a tuna a ranar 25 ga watan Oktoba ne aka samu rahoton sace yan matan da wata gungun masu garkuwa da mutane suka yi a lokacin da suke kan hanyar raba ma yan uwansu da kawayensu ankon bikinsu wanda ake gab da gudanar da bikin.

An sace yan matan ne a karamar hukumar Zurmi ta jahar Zamfara, kamar yadda mataimakin shugaban hukumar Abubakar Muhammad ya bayyana, inda yace an sace mutane bakwai a cikin kwanaki biyu, daga cikinsu har da tagwayen.

Daga baya suka bayyana cewa zasu kashe tagwayen matukar ba’a biya musu bukatarsu na biyan kudin fansa ba. Ba da dadewa ba aka sako yan matan bayan gudunmuwar da wasu yan siyasan jihar suka taimaka da kudin fansar naira miliyan 15.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel