Marigayi Shehu Shagari bai taba kiran kowa barawo ba - Shehu Sani

Marigayi Shehu Shagari bai taba kiran kowa barawo ba - Shehu Sani

- Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewa marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya, Alhaji Shehu Shagari bai taba kiran kowa da sunan barawo ba

- Sani ya kuma ce marigayin bai taba nuna cewa shi yafi wani tsarkaka ba

- Ya yabi Shehu Shagari a matsayin mutun mai gaskiya da amana

Shehu Sani, Sanata mai wakiltan yankin jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasar ya bayyana cewa marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya, Alhaji Shehu Shagari bai taba kiran kowa da sunan barawo ba sai dai nuni da yake yi ga cewar shi shugaba na gari ne a aikace lokacin da yake raye.

A wani rubutu da Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na twitter ya bayyana tsohon shugaban kasar a matsayin mutun mai gaskiya da amana wanda bai taba bayyana kansa a matsayin waliyi ba.

Marigayi Shehu Shagari bai taba kiran kowa barawa ba Shehu Sani
Marigayi Shehu Shagari bai taba kiran kowa barawa ba Shehu Sani
Asali: UGC

Ya ce: “Shugaban kasa Shehu Shagari bai taba kiran kowa da sunan barawo ba kuma bai taba kiran kansa a matsayin waliyi ba. Kawai dai yayi rayuwa ne da ya nuna cewa shi mutum ne mai gaskiya da amana kuma abun koyi. Shine farko kuma na karshe da ya kawo karshen jumhuriyya na biyu. Allah ya ji kan shi ya kuma sa shi a Aljannar Firdausi. Amin.”

Tsohon shugaban kasar dai ya rasu ne, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, ya rasu ne a babbar asibitin kasa da ke Abuja.

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji ta karyata rahotannin cewa Boko Haram sun kwace garuruwan Borno 6

A baya mun ji cewa Babban dan marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya, Alhaji Shehu Shagari ya bayar da bayani akan kwanakin karshe da mahaifinsa yayi a duniya.

Bala Shagari yace koda dai mahaifin nasa ya dade da daina magana saboda halin rashin lafiya, ya dade yana da burin ganin an binne shi a gidansa da ke garin Shagari, jihar Sokoto a duk lokacin da Allah zai amshi ransa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel